Kotun Katsina Ta Yi Watsi da Karar da Jiga-Jigan PDP Suka Shigar
- Katsina City News
- 10 Jan, 2025
- 364
Kotun Katsina Ta Yi Watsi da Karar da Jiga-Jigan PDP Suka Shigar
Wata babbar kotu a Jihar Katsina ta yi watsi da karar da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP suka shigar, suna kalubalantar yadda aka gudanar da zabukan shugabannin jam’iyyar a matakan mazabu, kananan hukumomi, da jiha a bara.
Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Mustafa Inuwa, tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar su takwas ne suka kai shugabannin jam’iyyar kara kotu bisa zargin hana wasu mambobin jam’iyyar samun fom na takarar shugabancin jam’iyyar.
Masu shigar da karar sun bayyana cewa sun kai karar ne a madadin wasu mambobin jam’iyyar 7,905 da suka nuna rashin jin dadinsu kan yadda aka gudanar da zabukan shugabannin.
Jam’iyyar PDP, ta hannun lauyanta, ta bukaci kotu ta yi watsi da karar, tana mai cewa kotu ba ta da hurumin sauraren irin wannan rikicin.
A yayin yanke hukuncinsa, mai shari’a Abbas Bawale ya yi watsi da karar bisa dalilin cewa kotu ba ta da hurumi kan rikice-rikicen da suka shafi zaben shugabannin jam’iyya, domin hakan rikici ne na cikin gida.
Mai shari’a Bawale ya ambaci wasu hukuncin kotuna daban-daban da kuma tanade-tanaden dokar zabe ta 2022, wadanda suka nuna cewa hurumin kotu ya takaita ne kan rikicin fidda gwani na jam’iyyun siyasa.
Game da ikirarin lauyan PDP cewa masu shigar da karar ba su kai koken nasu ga shugabancin jam’iyyar na kasa ba, mai shari’a Abbas Bawale ya ce kotu ta gamsu da cewa masu karar sun yi amfani da duk hanyoyin cikin gida wajen neman sulhu kafin su garzaya kotu.
Bayan hukuncin, lauyan masu shigar da karar, Barista Mustafa Shitu Mahuta, ya bayyana rashin gamsuwarsa da hukuncin kotu, tare da yin alkawarin daukaka kara a madadin wadanda yake karewa.