‘Yan bindiga sun yi Kwanton Bauna, sun kashe 'Yan Kwaminiti Wach da mutane da dama a Katsina
- Katsina City News
- 10 Jan, 2025
- 30
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane da dama a hare-hare da suka kai wa membobin kungiyar sa-kai ta Katsina da mazauna wasu kauyuka a ranar Talata.
Cikakkun bayanai game da harin sun fito fili a jiya, Alhamis
Shaidu sun shaida wa BBC cewa wadanda aka kashe sun fito ne daga kananan hukumomin Charanci, Safana, Kurfi da Kaita na Jihar Katsina.
Mazauna yankin da suka tattauna da jaridar Daily Trust sun ce adadin wadanda suka rasa rayukansu ya kai sama da 30.
Rahotanni sun nuna cewa wadanda aka kai wa harin suna dawowa daga wata ziyara ta ta’aziyya a garin Batsari ne lokacin da aka yi masu kwanton bauna.
An kai harin ne a kauyen Baure, wanda aka sani a matsayin mafakar ‘yan bindiga.
Wasu mazauna kauyen Barebari a karamar hukumar Safana, da suka nemi a sakaya sunansu, sun ce fiye da mutane 15 sun mutu a wurin harin.
“Baure kauye ne da aka sani a matsayin mafakar ‘yan bindiga. A ranar kasuwa abin ya faru, inda suka bi jama’a har gida suka kashe fiye da mutane 15, kamar yadda gawarwakin da muka gani suka tabbatar. Sun kona wasu gawarwakin, wasu kuma har yanzu ba a gano su ba. A farko, ba su bari mu dauki gawarwakin ba, amma daga bisani suka sassauta,” in ji wani mazaunin kauyen.
Wani mazaunin ya ce: “Mun samu damar ceto fiye da mutane 20. Wadanda aka kashe sun hada da mutanen Charanci, Burji, Jibiya da Kaita. A kalla mutane 25 aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da wasu har yanzu ba a san inda suke ba.”
Wani mazaunin da ya ce daya daga cikin wadanda aka kashe dan uwansa ne ya ce: “Daga cikin wadanda aka kashe akwai ‘yan sa-kai.
“Ba tare da saninsu ba, ‘yan bindigar sun riga sun shiga kauyen. Da suka hangi mutanenmu, sai suka buya a gidajen jama’a sannan suka bude wuta, inda suka kashe sama da mutane 30.
“Dan uwana yana cikin wadanda aka kashe, kuma yau (Alhamis) ne muka samu damar daukar gawarsa don binne ta, bayan da ‘yan bindiga suka hana daukar gawarwaki tsawon kwanaki biyu bayan afkuwar lamarin,” in ji shi.
“Wadanda aka kashe sun kasance membobin kungiyar sa-kai daga kananan hukumomi daban-daban, wadanda suka je yin ta’aziyya a kauyen Madaddafai kan mutuwar daya daga cikin membobinsu. Bayan ta’aziyyar, shugabanninsu sun koma gida, amma sauran sun yanke shawarar zuwa kauyen Baure, inda aka kai musu kwanton bauna.”
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina, Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da faruwar harin, amma ya ce: “Har yanzu muna tattara bayanai, kuma za mu bayar da cikakken bayani nan gaba kadan.”