Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Ƙasa NAHCON ta fara shirin aikin Hajjin 2025
- Katsina City News
- 10 Jan, 2025
- 21
Katsina Times
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta bayyana cewa tawagar hukumar karkashin jagorancin Shugabanta, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ta tafi kasar Saudiyya domin shirin aikin Hajjin 2025.
Sanarwar da Mataimakiyar Darakta mai kula da Sashen Labarai da Wallafa na NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar ta ce wannan ziyara ta fara ne a ranar 7 ga Janairu, 2025, bisa gayyatar Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya (MoHU).
Ta bayyana cewa manufar ziyarar ita ce domin shirye-shiryen sanya hannu kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) don aikin Hajjin 2025 da kuma kammala wasu shirye-shirye na aikin Hajjin shekara-shekara ga Musulmi.
"Ayyuka masu muhimmanci a yayin wannan ziyara sun hada da ganawar bangarorin biyu da kuma sanya hannu kan yarjejeniyar MoU don Hajjin 2025, wanda aka tsara a ranar 12 ga Janairu, 2025. Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Jakada Yusuf Maitama Tuggar, shi ne zai sanya hannu a madadin Najeriya," in ji ta.
Ta kara da cewa, tawagar za ta halarci bikin baje kolin kasa da kasa na Hajji (International Hajj Expo) da zai fara a ranar 13 ga Janairu, 2025, domin duba da kuma tantance masu samar da hidima ga alhazan Najeriya.