SANARWA TA MUSAMMAN DAGA OFISHIN MAI BA MAIGIRMA GWAMNAN JIHAR KATSINA SHAWARA AKAN HARKOKIN SIYASA.

top-news

A kokarin da yake na farfado da gamayyar kungiyoyi masu goyan bayan gwannatin Jihar Kataina, maiba Gwamna shawara akan harkokin siyasa, Rt.Hon Alhaji Umar Ya'u Gwajogwajo,  bisa sahalewar Maigirma Gwamna Malam Dr Dikko Umar Radda, na sanar da rushe shugabacin "Coalition of Political Groups", gamayyar kungiyoyin siyasa dake tallata manufofin Gwamnatin, tare da kafa kwamitin riko, karkashin shugabacin  Maigirma Tsohon Dantakarar Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina na riko,  karkashin jam'iyyar APC, Alh Yusuf Aliyu Musawa

Haka kuma, ana sanar da Shugabanin kungiyoyin Siyasa ,dana yankasuwa da masu sanaoi magoya bayan  jamiyyar APC  a Jihar Katsina cewa

 an fito da sabon fam  domin yima kungiyoyin  rigista karkashin  wannan inuwa, akan kudi naira dubu daya kacal.

Zaa fara Saida form din daga ranar Monday 13 ga wannan wata na Junairun 2025.

Zaku iya samun wannan Fam a Ofishin Kungiyar na wucin gadi dake Ofishin Mai ba Maigirma Gwamna shawara akan harkokin siyasa dake tsohon gidan Gwamnati, ko  a kananan Hukumomi. kuma zaku iya samun fam din a Ofishin Jam'iyyar APC na kowace Karamar Hukuma na Jihar Katsina .

Sanarwa daga 
Bashir Ya'u (Bershow)

Sakataren yada labarai  na rukon kwarya.