Najeriya ta bukaci majalisar dinkin duniya ta binciki yadda Boko Haram ke samun kudade da horo
- Katsina City News
- 09 Jan, 2025
- 68
Najeriya ta yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta gudanar da bincike kan yadda ake samar da kudade da horar da ‘yan ta’addan Boko Haram.
Daily Trust ta rawaito cewa Babban Hafsan Tsaro na ƙasar, Janar Christopher Musa, ne ya yi wannan kiran a wata hira da ya yi da Al-Jazeera kwanan nan.
Musa ya bayyana cewa akwai wata hanyar samun kudade ta duniya ga ‘yan ta’addan, inda ya jaddada bukatar Majalisar dinkin duniya ta shiga don gano asalin kudaden.
Janar din ya tambayi yadda ƴan ta’addan su ka samu damar tsayawa tsawon shekaru 15 suna ci gaba da kai hare-hare, tare da zargin hadin baki da ƙasashen duniya wajen ba su kudade, horo, da kayan yaki.
Da ya ke mayar da martani kan tambayar dalilin da ya sa Boko Haram ke ci gaba da sake kara karfi duk da ikirarin gwamnatin tarayya cewa an rage musu karfi, ya ce: “Matsalar ita ce, na yi tunanin mun yi magana da al’ummar duniya. Mu gano asalin kudaden. A halin yanzu, sama da mambobi 120,000 na Boko Haram sun mika wuya, kuma mafi yawansu sun zo da kudade masu yawa. Yaya suka same su? Ta yaya ake samun kudaden? Yaya aka horar da su? Yaya suka samu kayan aiki?
“Akwai bukatar shiga cikin wannan lamari domin mu gano inda kudaden suka fito. Wani al’amari ne na kasa da kasa, kuma ba mu da ikon sarrafa shi,” in ji shi.
Daily Nigeria Hausa