Matashin Dan Siyasa A Jihar Katsina, Musa Gafai, Ya Shirya Tsaf Domin Karɓar Katin Jam'iyyar APC A Mazaɓarsa
- Katsina City News
- 09 Jan, 2025
- 42
Sanannen matashin ɗan siyasa kuma ɗan kasuwa, Alhaji Musa Yusuf Gafai, ya tabbatar da shirinsa na shiga jam'iyyar APC cikin cikakkiyar niyya da ƙarfin gwiwa. Wannan mataki ya biyo bayan sauya sheƙarsa daga jam'iyyar PDP zuwa APC, wanda ya bayyana a matsayin matakin da ya yi saboda irin kyakkyawan hangen nesa da gwamna Malam Dikko Umar Radda ke nunawa wajen gina sabuwar jihar Katsina mai cigaba.
Wannan sanarwa ta fito ne daga ofishin yaɗa labarai na Alhaji Musa Yusuf Gafai, wanda ya bayyana a cikin wata takarda da aka raba wa manema labarai a satin nan. A cewar sanarwar, Alhaji Musa Gafai, wanda ya kasance tsohon daraktan tuntuba a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da gwamna a jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki domin cika burinsa na taimakawa wajen inganta rayuwar al'umma ta hanyar aiki tare da gwamna Radda da jam'iyyar APC.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Alhaji Musa Gafai zai karɓi katin zama cikakken ɗan jam'iyyar APC a ranar 1 ga watan Fabrairu, a mazabarsa ta Wakilin Yamma II da ke cikin garin Katsina. Wannan rana, kamar yadda jawabin ya bayyana, za ta kasance muhimmiyar dama domin tabbatar da shigarsa cikin tafiyar jam'iyyar APC tare da tabbatar da jajircewarsa wajen ba da gudunmawa ga cigaban jihar Katsina.
Haka zalika, Alhaji Musa Gafai ya yi kira ga matasa da sauran al’ummar jihar Katsina da su marawa gwamna Radda baya wajen ganin an cimma muradun da aka sanya a gaba na kawo ci gaba mai ɗorewa a dukkan fannoni. Ya kuma bayyana cewa, sauya shekar tasa ya samo asali ne daga gamsuwarsa da manufofin gwamnatin jihar da kuma irin kulawar da ake bai wa matasa wajen shigar da su a cikin tafiyar ci gaba.
A karshe, Alhaji Musa Yusuf Gafai ya tabbatar da cewa shirinsa na shiga APC ba kawai na siyasa ba ne, amma wani yunkuri ne na tabbatar da cewa jihar Katsina ta samu jagoranci nagari wanda zai ba da damar gina kyakkyawar makoma ga al'umma baki ɗaya. Wannan matakin ya jawo hankalin jama'a a jihar, musamman matasa, wadanda ke kallon shi a matsayin jagoran cigaba da kishin kasa.
Karɓar katin jam’iyya daga Alhaji Musa Yusuf Gafai zai zama wani sabon babi a tafiyar siyasar jihar Katsina, da kuma ci gaba ga jam’iyyar APC a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya.