Mata Da Miji Sun Zama Farfesa A Rana Daya A Jami'a Daya.
- Katsina City News
- 07 Jan, 2025
- 63
Jami’ar Bayero da ke Kano, BUK, ta kafa wa wasu ma'aurata babban tarihi, bayan da ta ba su matsayin Farfesa a lokaci guda.
Farfesa Suleiman Mainasara Yar'adua da matarsa Farfesa Aisha Haruna, sun taka wannan babban matsayin nasu ne a lokaci guda, kuma a daidai lokacin da suka shafe shekaru 24 da aure, suna aikin koyarwa da aka bayyana a matsayin mai cike da sadaukarwa a jami'ar, Jaridar Taskar Labarai ta ruwaito.
Taka wannan matsayin nasu a lokaci guda, manuniya ce ga 'yan baya bisa ga irin kwazo, sadaukarwa, da kuma kwarewarsu a fannin Iliminsu.
An bayyana Farfesa Mainasara 'Yar'adu'a a matsayin masani a fannin Sadarwar Ci Gaban Ƙasa "Development communication", wanda ya bada gudummawa sosai a fannin ta hanyar bincike da wallafe-wallafe masu ban sha'awa da matukar tasiri.
Ita ko Uwargidan tasa, Farfesa A’isha Haruna, wata shahararriyar masaniya a fannin Shari’a ta jama’a "Public Law" a turance, an bayyana ta a matsayin wacce ta ci gabantar tare da bunkasa fannin nata ta hanyar mai da hankali kan 'yancin dan Adam da nazarin jinsi.
Bugu da kari, an kuma bayyana irin nasarorin da suka samar da cewar ba kawai ya tsaya ga Jami'ar ta BUK ba, a'a har ma da bunkasa Ilimi domin al'umma ta amfana. A dalilin haka, Jami'ar ta amince da su a matsayin wadanda suka sadaukar da bada gudummawa wajen bunkasa ilimi da samar da gurabun karatu.
Ma'auratan, Farfesa Mainasara 'Yar'adu'a da Ai'sha Haruna sun bayyana jin dadinsu bisa ga wannan karramawa, inda suka jaddada aniyarsu na ciyar da fannin nasu gaba tare da kara zage damtse wajen bayar da gudummawa don karin ci gaban Jami’ar.
"Wannan ci gaban zai sa mu ci gaba da jajircewa a jami'ar," in ji su a wata fira.
Har wayau, Jami’ar ta taya ma'auratan murna, ta kuma yaba kwazonsu wanda hakan ya zama abin koyi ga al'umma wajen samun nasara a fagen ilimi.