'Yan Ta'adda Sun Kashe Shugaban Miyetti Allah, Sun Sace Matansa da 'Yarsa
- Katsina City News
- 05 Jan, 2025
- 218
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Wasu da ake zargin 'yan ta’adda ne sun hallaka mukaddashin shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar Katsina, Alhaji Amadu Surajo, tare da kashe wasu mutum uku da jikkata wasu da dama.
Lamarin ya faru ne a daren Asabar zuwa safiyar Lahadi a kauyen Mai Rana da ke karamar hukumar Kusada ta jihar Katsina.
Bayanai sun nuna cewa ‘yan ta’addan sun sace matan mukaddashin shugaban guda biyu da daya daga cikin ’ya’yansa mata, wadda daliba ce a wata jami’ar gwamnati a Najeriya. Sai dai majiya ta ce daga baya an saki matar farko.
Kafin rasuwarsa, Alhaji Surajo shi ne sakataren kungiyar Miyetti Allah a jihar Katsina, amma an nada shi mukaddashin shugaban kungiyar bayan batan shugaban kungiyar a jihar, Alhaji Munnir Lamido, a watan Yunin bara.
Lamido ya bace ne ranar 23 ga watan Yuni a kan hanyarsa daga Katsina zuwa Kaduna, bayan ya sanar da iyalansa cewa ya tsaya cin abinci a Zariya. Tun daga nan ba a sake jin duriyarsa ba, sai dai daga baya an gano motarsa da wayoyinsa a kusa da Maraban Jos.
A wannan sabon harin na daren Asabar, an ruwaito cewa jami’an tsaro sun dira yankin domin tabbatar da tsaro da kuma binciken al’amarin.
Za a yi jana’izar Alhaji Surajo da sauran wadanda suka rasu da safiyar Lahadi bisa ga koyarwar addinin Musulunci, yayin da wadanda suka jikkata ke karbar magani a asibiti.
Ko da yake ana fama da matsalar tsaro a wasu kananan hukumomi a jihar Katsina, karamar hukumar Kusada ba ta cikin wuraren da ake yawan samun irin wadannan hare-hare, lamarin da ya haifar da tambayoyi daga wasu bangarori kan ko harin ya wuce kaddamarwa na 'yan ta’adda kawai.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, bai amsa tambayoyin manema labarai game da lamarin ba a lokacin hada rahoton.