Ƴansanda sun tabbatar da mutuwar mutane tara a wani rikici a Jigawa

top-news

Rundunar ƴansanda ta Jihar Jigawa, a yau Asabar, ta tabbatar da cewa rikicin da ya afku tsakanin al’ummomi da ya faru a jiya Juma’a ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tara, tare da jikkatar wasu mutane hudu.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa rikicin  ya faru ne a karamar hukumar Miga ta jihar, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, tare da jikkatar wasu da yawa da aka kwantar a asibiti.

Sai dai kuma kakakin rundunar Jihar, SP Shiisu Adam, a wata sanarwa, ya tabbatar da cewa rikicin ya afku ne tsakanin wasu ƙauyuka a karamar hukumar Jahun. 

Ya kara da cewa, mutane tara sun mutu yayin da wasu 4 ke ci gaba da samun kulawa a asibiti.

Ya ce, “A ranar 03/01/2025, mun samu labari daga kauyen Gululu a karamar hukumar Miga cewa wasu bata-gari da ake zargin Fulani ne sun kutsa cikin wani shago sun saci zoɓarodo da wasu kayan abinci.

“Sai wata m tawagar mazauna kauyen (Hausawa) su ka bi sawun takun su zuwa sansanin Fulani a kauyen Yankunama, karamar hukumar Jahun.

"Da su ka hango tawagar, sai Fulani  su ka fara harbin su da kwari da baka, wanda ya jikkata mutane hudu sosai. 

Wannan ya sa mazauna kauyen suka far wa Fulani, suna kona gidajensu a wurare daban-daban a kananan hukumomin Miga da Jahun.” in ji shi.

Sai dai Shiisu ya tabbatar da cewa tuni aka shawo kan lamarin kuma ƴansanda na ci gaba da bincike.