Malamin Islamiya Ya Yi Wa Dalibarsa Ciki a Ibadan
- Katsina City News
- 03 Jan, 2025
- 111
Wani malamin Islamiya da aka fi sani da Malam Akibu Idris, wanda aka yi wa lakabi da “Malam Mai Kyalkyali,” ya shiga cikin rikici bayan da aka tabbatar da cewa jaririyar da dalibarsa Maryam Ibrahim ta haifa, diyar sa ce. Wannan batu ya biyo bayan sakamakon gwajin DNA da Hukumar DDC ta Jihar Oyo ta gudanar, wanda ya tabbatar da cewa jinin jaririyar ya dace da na Malamin har kashi 99.99%.
Idan ba a manta ba, Jaridar Aminiya ta wallafa labarin Malamin a ranar 9 ga watan Agusta na shekarar bara, inda aka zarge shi da yin fyade ga dalibansa 'yan mata guda bakwai, ciki har da Maryam Ibrahim. Sai dai Malamin ya rantse da Alkur'ani cewa bai taba yin lalata da ita ba.
Lokacin da wannan lamari ya faru, Unguwar Sabo da ke birnin Ibadan, wadda Hausawa suka fi yawa, ta cika da hargitsi. Malamin ya tsere bayan da wasu daga cikin 'yan uwan Maryam suka lakada masa duka. Fusatattun jama’a, ciki har da matan aure da 'yan mata, sun yi dafifi a gaban Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ali Dahiru Zungeru, suna neman daukar mataki kan Malamin.
Gamayyar kungiyoyin Hausawa masu fafutukar kare hakkin dan Adam, karkashin jagorancin Malam Nafi'u Hamisu, sun shigar da korafi a Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Jihar Oyo. Hukumar ta yanke shawarar jiran lokacin da Maryam za ta haihu domin gudanar da gwajin DNA.
Bayan haihuwar jaririyar, hukumar ta gayyaci Malamin don yi masa gwajin DNA, wanda ya tabbatar da cewa shi ne uban jaririyar. Hukumar ta mika Malamin ga jami’an tsaro na Civil Defence, wadanda suka tsare shi har zuwa lokacin gabatar da shi a gaban kotu.
Bayan haka, wasu daga cikin dangin Malam Akibu sun nemi a yi sulhu kafin kai lamarin gaban kotu. An cimma yarjejeniya a Babban Masallacin Sabo, inda Malamin ya amince cewa shi ne uban jaririyar. Yarjejeniyar ta bukaci Malamin ya biya dukkan kudaden da aka kashe wajen haihuwar jaririyar, tare da daukar nauyin kulawar jaririyar.
A lokacin da ake kulla yarjejeniyar, Malamin ya amince cewa ya yi lalata da Maryam, amma ya danganta hakan ga aikin shaidan. Ya nemi gafara daga jama’a tare da bayyana cewa yana fatan a yafe masa. Duk da haka, Malamin ya musanta wasu daga cikin zarge-zargen da ake masa, ciki har da yin amfani da maganin gusar da hankali kan wasu dalibai, da zargin kasancewa mabiyin akidar Shia.
Ya ce:
“An fi karfina ne aka yi min taron dangi. Gaskiya za ta bayyana ne gobe kiyama.”
A wata hira ta waya da Aminiya, Malamin ya ce an kulla masa sharri kuma zai bayyana gaskiyar lamarin nan gaba. Ya ce mabiyin Darikar Tijjaniya ne, ba Shia kamar yadda ake zargi.
Rahoton Aminiya ya tabbatar da cewa Malamin ya dade da barin Ibadan bayan wannan al’amari. Wannan labari ya dauki hankalin jama’a sosai, musamman mazauna Unguwar Sabo.
Lamarin ya kasance darasi ga iyaye, malamai da duk masu ruwa da tsaki a harkar ilimi. Duk da sulhu da aka cimma, ana sa ran jami’an tsaro za su tabbatar da adalci ga dukkan bangarorin.