Bello Turji Matacce Ne -Rundunar Tsaro
- Katsina City News
- 03 Jan, 2025
- 53
Daga Sagir Kano Saleh
Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana cewa jagoran 'yan ta’adda da ya addabi jihohin Sakkwato da Zamfara, Bello Turji, matacce ne kawai da ke yaudarar kansa.
Mai magana da yawun rundunar sojin, Manjo-Janar Edward Buba, ya bayyana cewa, kasancewar Turji na rayuwa domin yaƙi, aika shi lahira ya zama dole don samar da zaman lafiya mai ɗorewa.
A cikin jawabin da ya gabatar kan nasarorin da rundunar ta samu a shekarar 2024, Manjo-Janar Buba ya ce sojoji za su ƙara tsaurara farmakin da suke kaiwa maboyan 'yan ta’adda, domin kawo ƙarshen ayyukansu cikin gaggawa.
“A bana, sojojinmu sun aika dubban 'yan ta’adda, kwamandojinsu, da mayakansu barzahu. Mun tabbatar cewa sauran jagororinsu za su bi sahun waɗanda suka rigaya zuwa lahira,” in ji shi.
Ya kuma ƙara da cewa:
“Turjimatacce ne. Ba da jimawa ba zai bi sahun sauran fitattun 'yan ta’adda da muka kashe a bana, irin su Halilu Sububu, Dutse Mainasara, Mallam Saleh Umaru, Mohammed Amadu, Abubakar Musa, Adamu Tanko Ibrahim, Yellow Dogon Rakumi, Isiya Boderi, da Alhaji Baldu.”
Manjo-Janar Buba ya jero sunayen sauran jagororin da suka rage a tsakanin 'yan ta’addan, ciki har da Usman Modi Modi, Kachalla Halilu, Kachalla Tukur, Amir Ibrahim Bukar, Saidu Hassan Yellow, Buba Kachalla Bukar, Bakura Jega, da Abba Tukur, yana mai cewa ba za su tsira ba.
A cewarsa, a shekarar 2024, rundunar ta samu nasarar sa wasu daga cikin 'yan ta’adda su mika wuya tare da iyalansu, yana mai ƙara jaddada cewa sojoji za su ci gaba da ƙoƙarin kare Nijeriya da murkushe duk wata barazanar ta’addanci.
(NAN)