KIWON LAFIYA: Cizon Kare da Alamomin Cutar
- Katsina City News
- 02 Jan, 2025
- 112
Idan kare mai ɗauke da cutar (virus) ya ciji mutum, cutar za ta shiga cikin jikinsa. Wannan na iya haifar da rashin son ruwa ko tsoro daga gareshi. A wasu lokuta, idan ya ga ruwa, zai shiga cikin yanayin hauka.
Alamomin Cutar Cizon Kare
1. Kasalar jiki gaba ɗaya.
2. Rashin iya numfashi sosai tare da ɗalalar miyau daga baki.
3. Fizge-fizgen jijiyoyin makoshi.
4. Zazzabi mai tsanani.
5. Mutuwar wani sashen jiki daga baya idan mutum ya tsananta.
Rigakafin Kamuwa da Cutar Cizon Kare
1. Kebe karnukan da aka san suna ɗauke da kwayoyin cutar domin hana yaɗuwar cutar.
2. Yi wa karnuka allurar rigakafi domin kariya daga kamuwa da cutar.
3. Samar da allurar rigakafi da wuri idan an samu annobar cutar a karnuka.
4. A kashe karnukan da aka tabbatar suna ɗauke da cutar, sannan a binne su daidai gwargwado don hana yaɗuwar cutar.
Lura: Rigakafi da sauri na iya kare rayuwa, don haka yana da mahimmanci a ɗauki mataki nan take idan aka ji cizon kare mai dauke da cutar.
Daga Littafin Kula da Lafiya na Safiya Ya'u Yemal