Gidan Man Imrana Nig Nigerian Limited Dake Bisa Titin Fatima Shema Cikin Garin Katsina, Ya Koma Gidan Man NNPC Mega Station.
- Katsina City News
- 01 Jan, 2024
- 99
Muhammad Ali Hafiziy (Katsina Times)
A ranar Litinin 31 ga watan Disamba na shekarar 2024, aka canza ma gidan man Imrana Nigerian Limited, dake bisa titin Fatima Shema suna zuwa gidan man NNPC Mega Station .
Taron ya gudana ne a harabar gidan man, gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya samu wakilci daga wajen kwamishina na ma'aikatar ciniki da masana'antu na jihar Katsina, Hon Adnan Na Habu, Alhaji Abba Sani, mai kula da gidan mai na shiyar Arewa masu Yamma, Sakatare, Alhaji Umar Yabo mai kula da gidajen mai na NNPC na jihar Katsina, wakilci daga magajin garin Katsina, ta hanyar wakilin kudu, da sauran yan kasuwa, yan siyasa da alummar gari.
A jawabin da ya gabatar a wajen taro, shugaban dake kula da gidajen man NNPC na jihar Katsina, Alhaji Umar Yabo, "Babban kudurinmu shine muga lungu da sako alumma suna samun mai cikin sauki kuma mai inganci, wannann dalilin me ya sa kamfanin NNPC ya sanya mu zagayawa domin samun gidajen man da zaa maida sun NNPC, Alhamdulillah cikin shekara daya munyi nasarar kawo ma NNPC gidajen mai guda shida" inji shi.
Shima a jawabin da ya gabatar kwamishinan ciniki da masana'antu, ya jinjina ma gidan man Imrana Nigerian Limited wajen bayar dashi da yayi domin samar da cigaba a cikin jihar Katsina, "Babu shakka bude wannnan gidan man ya bude wani sabon shafi na cewa da talakawan jihar Katsina, da gwamnatin jihar Katsina da yan kasuwa, ana tafiya tare domin ganin an kawo ma alumma saukin rayuwa".