Jami'ar Al-qalam dake Katsina ta yabawa Gwamna jihar a kokarin sa na kewaye makarantar baki dayanta
- Katsina City News
- 31 Dec, 2024
- 75
Mataimakiyar Shugaban Jami'ar maikula da sha'aninin mulki, Furofesa Amina Muhammad Sani ce ta jinjina ma Gwamna Dikko Umaru Radda bisa wannan katafaren aiki wanda yanzu haka yana gudana kamar yadda ya yi alkawari.
Furofesa Amina Sani ta fadi haka ne a wajen wani taron karfafa zumunci wanda daliban Jami'ar da suka kammala karatu a shekara ta 2012 suka shirya a zauren taro na sashen ICT dake Makarantar.
Sai dai kuma ta roki Gwamna Dikko Umaru Radda da ya taimaka ma Jami'ar wajen ceto Tsangayar nazarin rayuwar danadam daga durkushewa saboda Karancin dalibai.
Mataimakiyar Shugaban Jami'ar ta yi bayanin cewa yanzu haka sassan dake a karkashin Tsangayar da suka hada da na Nazarin
Turanci da na Nazarin Larabci da na Hausa da na Harkokin Addinin Musulunci, suna matukar faskatar karancin dalibai wanda idan ba a yi hattara ba, hakan zai iya kaiwa ga rufe su baki daya.
Ta yi nuni da cewa dukkan sassan suna bada muhimmiyar gudummuwa ga cigaban jihohin Arewa musamman Katsina da Kano da Jigawa da Zamfara wajen samar da Malaman Makaranta da Alkalai da sauran kwararrun Ma'aikatu.
Furofesa Amina ta ce kasancewar Jami'ar ta farko ta al'umma mai zaman kanta tana bukatar gwamnatoci da sauran masu sukuni da su taimaka wajen tura dalibai da daukar nauyin su don yin karatu a wadan nan sassan.
A nasa jawabi, Mataimakin Shugaban Majalissar Dokoki ta Jihar Katsina, Hon. Abduljalal Haruna ya bayyana cewa karo na uku ke nan yana daukar nauyin dalibai bibiyu daga mazabarsa wadanda suke yin karatu a Jami'ar.
Hon. Runka wanda shi ma na cikin tsaffin daliban da suka shirya taron ya ce ya kuma yi hanya da wasu takwarorin aikinsa suka yi karatu a Jami'ar ta Alqalam.
Danmajalissar ya sha alwashin cigaba da bada gudunmuwarsa ga cigaban Makarantar tare da kira ga jagororin da suka shirya taron karo na farko da su yi kokarin mayar da shi na shekara - shekara.
Da yake jawabi shugaban kwamitin riko na daliban na 2012 Dr. Nuruddeen Gidado Yanhoho ya yaba ma mahalarta taron musamman wadanda suka bada gudummuwa ta kowace fuska don ganin taron ya yi nasara.
Sauran wadanda suka yi jababi sun hada da Dr Aminu Yakubu da Dr Ahmed Danmaigoro da Dr Mustapha Mairali da Malam Salisu Ibrahim Kazaure da Malam Sagir Gambo Saulawa da Hajiya Hadiza Usman Umbule.
Daga cikin abinda ya kayatar da taron har da bada lambobin yabo ga wasu daga cikin Malaman da suka koya masu.