Dan Majalisar Tarayya Na Mashi Da Dutsi Ya Bude Dakin Gwaje-gwaje Mai Sunan shi a Katsina
- Katsina City News
- 30 Dec, 2024
- 96
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Lahadi, 29 ga watan Disamba, 2024, Dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Mashi da Dutsi a jihar Katsina, Honorable Salisu Yusuf Majigiri, ya kaddamar da Dakin Gwaje-gwaje na kimiyyar lafiya a makarantar GIAL da ke Katsina. Wannan dakin gwaje-gwajen, wanda aka sanya wa suna "Hon. Salisu Yusuf Majigiri Laboratory," mallakin tsohon dan majalisar tarayya, Honorable Hamisu Gambo Danlawan Katsina ne.
Da yake jawabi yayin bikin kaddamarwar, tsohon dan majalisar, Hon. Hamisu Gambo, ya bayyana dalilin sanya sunan Hon. Salisu Yusuf Majigiri a dakin gwaje-gwajen, yana mai cewa:
"Mun zabi wannan suna ne saboda muhimmancin da Hon. Salisu Majigiri yake da shi ga al’ummar jihar Katsina, musamman yadda ya mayar da hankali wajen bunkasa fannin kiwon lafiya. Wannan shine dalilin sanya sunayen wasu muhimman mutane a wasu gine-ginen makarantar, kamar su tsohon shugaban kasa, marigayi Malam Umaru Musa Yar’adua; tsohon gwamnan jihar Katsina, Malam Ibrahim Shehu Shema; tsohon gwamna Malam Aminu Bello Masari; da kuma sunayen sarakunan Katsina da Daura. Wannan hanya ce ta nuna godiya ga irin gudunmuwar da wadannan shugabanni suka bayar ga jihar da kasa baki daya."
A nasa bangaren, Hon. Salisu Yusuf Majigiri ya nuna farin cikinsa da wannan karramawa. Yace, “Wannan abu ya tuna mini shekaru 32 da suka gabata lokacin da nake karatun fannin kiwon lafiya. Yanzu na fahimci cewa ilimin da na samu ya yi tasiri matuka, ganin an sanya sunana a wani gini da ke da alaka da kiwon lafiya. Wannan abu zai kara mini kwarin gwiwa wajen tallafa wa matasa su samu ilimi da horo a wannan fanni don inganta al’umma.”
Hon. Majigiri ya yaba da kayan aikin zamani da ya gani a dakin gwaje-gwajen, tare da jinjina wa malamai masu kwarewa a fannin koyarwa. Ya ce, “Na dade ban ga kayan aiki na zamani irin wannan ba. Kuma malamai suna bayani cikin fahimta, abin da ya tabbatar mini cewa makarantar tana tafiya bisa tsarin da ya dace.”
A karshe, Hon. Majigiri ya yi alkawarin ci gaba da taimaka wa makarantar GIAL a duk lokacin da bukata ta taso. Ya bayyana cewa tallafawa irin wadannan makarantu abu ne mai muhimmanci domin bunkasa fannin kiwon lafiya da ilimi a jihar Katsina da ma Najeriya baki daya.
Wannan bikin kaddamarwar ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na jihar, wadanda suka yaba da kokarin da aka yi wajen samar da wannan dakin gwaje-gwaje wanda zai taimaka wajen bunkasa ilimi da kiwon lafiya a jihar Katsina.