An Kaddamar Da Sabbin Shugabannin Kasuwar Chake (Hi-Mata Market) Dake Cikin Garin Katsina
- Katsina City News
- 29 Dec, 2024
- 123
A ranar Asabar, 28 ga Disamba, 2024, an ƙaddamar da sabbin shugabannin Kasuwar Chake, wanda aka fi sani da Hi-Mata Market, bayan karewar wa'adin shugabannin da suka shude.
Shugaban Kwamitin Gudanar da Zaɓen, yayin jawabin sa, ya yaba wa matasan kasuwar bisa ƙoƙarinsu na kawo ci gaba da sauyi mai kyau ga kasuwar. Mambobin kwamitin sun kuma bayyana gamsuwarsu kan sahihancin zaɓen da aka gudanar.
Sabon shugaban kasuwar, Saminu Aliyu, a jawabinsa jim kaɗan bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen, ya gode wa Allah bisa wannan nasara, sannan ya bayyana kudurorinsa na inganta kasuwar da samar da kyakkyawan yanayi ga 'yan kasuwar. Ya ce za su yi aiki tare da gwamnati domin tabbatar da ci gaba ga kasuwar da ma jihar baki ɗaya.
Sabbin shugabannin da aka rantsar sun haɗa da:
- Saminu Aliyu – Shugaban Kasuwa
- Dahiru Tijjani Sa’albarka – Mataimakin Shugaba
- Da Sauran shugabanni guda takwas da ke dauke da nauyi a fannonin gudanar da kasuwar.
Asalin Kasuwar Hi-Mata tana tsakiyar birnin Katsina, kuma ta samo asali tun farkon shekarun 1980. Kasuwar ta amshi sunanta daga wata mace mai suna "Hi-Mata," wadda gidanta yake kusa da filin bugu. Ta yi suna wajen sayar da kayan abinci kamar rogo, ganyen kwado, kulikuli, da makamantansu a gefen hanya. Wurin ya ci gaba da bunƙasa har ya zama wata ƙaramar kasuwa mai matuƙar amfani.
A shekarar 1998, kasuwar ta samu cikakkiyar matsayi a matsayin kasuwa, biyo bayan matsalar da tsohuwar kasuwar Katsina ta fuskanta, wanda ya sa gwamnati ta gina sabuwar kasuwa a hanyar Dutsin-Ma. Rashin isassun runfuna da kuma nisan sabuwar kasuwar daga cikin gari ya ja hankalin wasu 'yan kasuwa zuwa kasuwar Hi-Mata domin gudanar da harkokin su.
Kasuwar Hi-Mata na ci gaba da taka muhimmiyar rawa a harkokin kasuwanci na jihar Katsina, inda take zama wata kafa ta tallafawa tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga matasa.