Muna zaman lafiya da kamaru da Chadi da duk kasashen Africa Don haka ba zamu samu matsala da Kasar Niger ba -Ribadu
- Katsina City News
- 27 Dec, 2024
- 81
Babban mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribaɗu ya bayyana cewa zarge-zargen da shugaban ƙasar Niger na mulkin soja yayi kan Najeriya zarge-zarge ne waɗanda ba su da tushe balle makama, hasali ma ya ba su mamaki domin kuwa Najeriya ba ta nufin Niger da sharri kuma ba za su so wata masifa ta faɗa mata ba, kamar yadda Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.
A cewar Ribaɗu, "Najeriya ba ta da fitina ko rashin zaman lafiya da ƙasashe maƙwabta. Muna zaman lafiya da Kamaru, muna zaman lafiya da Chadi, muna zaman lafiya da Benin, ya za a yi kuma a ce wai za mu samu matsala da Niger ? Ta ina za a ce Najeriya ce za ta ba wa wata ƙasa dama ta zo ta zauna don ta kawo wa Niger hari ko fitina, ta ina ? Najeriya ba ta da wannan tarihin na ba wa ƙasashen waje dama su zo su zauna a cikinta". In ji shi.
Mai ba wa shugaban ƙasar shawara, ya kuma ƙara da cewa "Ko da Ingila da suka yi mana mulkin mallaka ko sau ɗaya ba su taɓa cewa wai za su kawo sojojinsu su zo su zauna a Najeriya ba. Amerika ma ba yadda ba ta yi ba amma ba mu yarda ba. Sai da muka ce ba mu yarda ba sannan suka je Niger ta ba su dama daga baya suka kore su. Ba ma Niger ba duk ƙasashen da Faransa suka yi wa mulkin mallaka haka suka yi ta yi amma ba mu taɓa yarda da haka ba". Ya ce.
Ya cigaba da cewa, "amma yanzu idan sojojin Niger suna faɗa da Fáraɲsa ba dole mu ma mu yi fáɗa da Faraɲsa ba kamar yadda ba ma faɗa da kowace ƙasa a Duniya. Guraren da shugaban ƙasar Niger ya ambata a Najeriya muna roƙon ƴanjarida da al’umma ku je ku duba ko akwai wasu baƙi kowane irin baƙo ma balle kuma a ce Faransa. Muna tabbatarwa mutanen Niger cewa Najeriya ba za ta taɓa zame musu matsala ba. Najeriya ba za ta taɓa yi wa Niger zagon ƙasa ba". Ya ce.
Malam Nuhu Ribaɗu ya kuma ƙara da cewa "Ya kamata Niger su fahimci cewa Najeriya ba matsala ba ce, ƴaɲ ta’áddaɲ nan su ne mutanen da suka matsa mana, duk abin da suke yi a Niger su na yi a Najeriya, mu haɗa kai mu yaƙe su. Mutanen Niger su sani cewa duk abin da ya taɓa ɗaya ya taɓa ɗaya, mutane ɗaya muke ba yadda za a yi a ce wai Najeriya ce za ta taimaka wa ƴan ta’adda har su zo su kawo wa Niger hari, ya kamata shugabanni su duba wannan. Kuma ya kamata su sani idan sun canza Faransa sun kawo wasu to suna kawo wata matsalar ne ta gaba, bai kamata su bar wasu mutanen suna maye gurbin Faransa ba. Duk wanda zai zo maka zai zo maka ne yanzu a matsayin aboki gobe ya zame maka masifa. Kamar yadda muka faɗa musu tun da kafin Amerika ta zo ta buɗe musu sansani mun faɗa muku kar ku yi, sun bayar amma yanzu sun gani. Yanzu ma muna bayar da shawara ku rabu da su Najeriya su ne ƴan’uwanku, ku dawo ku yi aiki tare". Ya ce.
Ya jaddada muhimmancin haɗin kai da aiki tare a tsakanin ƙasashen biyu domin samun nasarar murƙushe ƴan’ta’adda. "Akwai kasuwanci ba laifi, amma wani ya zo yayi amfani da mu dan ya musgunawa ƴan’uwanmu ba zai iyu ba. Abin da kake gani yanzu ko muna mu’amala da Faraɲsa ban da maganar kasuwanci da zamantakewar zaman lafiya da kowa a Duniya ba abin da Najeriya ta sa a gaba fiye da wannan abun. Muna neman ƴan’uwa su zo mu yi aiki tare . Ƴan Niger su sani cewa Najeriya ba ta da matsala da kowa a Duniya. Shugabannin kuma su sani in dai ana son a taimakawa mutane to su zo a yi aiki tare". Cewar Malam Nuhu Ribaɗu, babban mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro.