Kungiyar AFAN Ta Yaba wa Gwamna Radda bisa Raba Tallafi Noma ga Manoma a Katsina
- Katsina City News
- 24 Dec, 2024
- 164
Kungiyar manoma ta Najeriya (AFAN), reshen jihar Katsina ta yaba wa gwamna Dikko Umar Radda na jihar bisa raba ma manoman jihar tallafin kayan aikin gona mafi yawa a tarihin jihar.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar ta AFAN a jihar, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-gwajo, da aka rabawa manema labarai a Katsina ta ce tallafin noma shi ne irinsa mafi girma a tarihin jihar Katsina da ma Najeriya bakin daya.
Sanarwar ta lissafa kayayyakin da aka raba wa manoman da suka hada da tireloli 80 na takin zamani mai dauke da buhu 48,000, da injinan huda guda 4,000, da famfunan ban-ruwa masu amfani da hasken rana guda 4,000 wadanda kudinsu ya kai Naira biliyon 8.3.
“Manoma a jihar Katsina sun fara noman ranin banana kara dama domin wannan gagarumin tallafin da gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda ta samar musu.
“Wannan shine karon farko da mambobinmu suka samu tallafi mai yawan gaske, kuma wannan tallafin zai inganta samar da abinci a lolacin noman ranin da muka shiga yanzu.
“Taki tirela tamanin wanda Gwamnatin jihar ta Samar zai bunkasa yawan amfanin da ake samu a kowace kadada tare da kawar da matsalar samun taki a tsakanin manoma.
“Gwamnatin jihar Katsina ita ce ta sayo famfunan ban-ruwa masu amfani da hasken rana da injinan hu'da da na feshi kuma za a sayar wa manoma su ne a kan farashi mai rangwame domin a tallafa wa manoma a fadin jihar.
“Wannan tallafin ya dace da kudurin gwamnatin Malam Dikko Umar Radda na bunkasa harkar noma, kasancewar shi mai shedar karatun digirgir a fannin aikin gona, kokarinsa ya taimaka wajen bunkasa wannan fannin a kasa da shekaru biyu da yayi a matsayin gwamna.
Alhaji Ya'u Umar Gwajo-gwajo ya kuma hori manoman da za su ci gajiyar kayayyakin tallafin su guju sayar da su, ya bukace su su yi amfani da kayan wajen inganta nomansu, musamman noman rani da ake ciki yanzu