ZIYARAR BAZATA DA GWAMNA RADDA KE KAI WA ASIBITOCI ZAI IYA INGANTA FANNIN LAFIYA : Inji wani Danjarida a katsina
- Katsina City News
- 23 Dec, 2024
- 83
....Ayi binike akan tsarin KATHCIMA.
.....Tagwaye biyu sun mutu bisa zargin sakaci.
Daga wakilinmu.
@ Danmasani online Redio
Mai kamfanin' Gidan Radio Danmasani Online Abubakar Ayuba Masanawa ya yaba da ziyarar bazata da Gwamna Dikko Radda ke kaiwa Asibitocin da ke jihar katsina, ko a ranar 21 na wannan watan Gwamnan ya kai irin wannan ziyara ga Asibitin koyarwa na Gwamnatin Tarayya dake garin Katsina inda ya duba marasa lafiya da kuma hada hannun da hukumar Asibitin don inganta lafiyar majinyata.
A cewar Masanawa, wannan zai iya rage asarar rayuka da akeyi a bisa dalilai masu nasaba da sakacin ma'aikatan lafiya da karancin kayan aiki. Sannan ya inganta tsare- tsare da ke taimakawa kiwon kafiya.
A ranar 16 na wanna watan na Disamba ne Masanawa ya rasa Tagwayensa biyu da aka haifamasa a dalilin matsalolin dake da dangantaka da tsarin kiwon lafiya. Mahaifin Tagwayen wanda Danjarida ne kuma Ma'aikaci a ma'aikatan yada labarai ta jihar Katsina, ya kasance yana bisa tsarin kiwon lafiya da ake cire wani kaso daga albashin ma'aikata don kula da lafiyarsu.
Wannan tsarin akwai matakin farko wanda ma'aikaci da iyalansa za su sami kula daga asibiti, yayin da suke fama da kananan lalura kamar zazzabi ba tare da an tuntubi ma'aikatarsu ba, ya yin da shi kuma na mataki na biyun na manyan lalura ne kamar haihuwa, karaya da sauran su, inda a wannan karon sai ma'aikatar da ma'aikaci ke aiki ta turo da sakon bada izini ( wato Katsina State Contributory Healthcare Management Agency.)
"A yayin da watan haihuwar matar tawa ya kusa sai hukumar Asibitin ta shaida mana cewa, haihuwa na cikin mataki na biyu kuma ba za su amshi majinyaci a wannan matakinba saboda bashi da suke bin ma'aikatar tattara kason albashin jinyar ma'aikata ( Katsina State Contributory Healthcare Management Agency).
Don haka sai suka nemi muzo mu karbi takarda zuwa wani asibiti na gaba" In ji Masanawa
''Kafin ranar da yakamata in je, sai lalura ya kama matata na juyewar jariran a ciki, don haka na hanzarta zuwa karbar takardar da za ta bani damar tafiya babban Asibitin Gwamnatin jihar Katsina.
A wannan Asibitin Gwamnati, nasa hannun kan ayi aiki wa matata amma da aka auna sai suka ce in suka yi aiki dole sai an sa yaran a kwalba saboda basu kai lokacin haihuwa ba, kuma basu da wannan kwalba. '
' Masanawa ya ci gaba da cewa' Wannan dalilin ya sa suka tura mu Asibitin Turai Yaradua mallakar Gwamnatin jihar Katsina. Babban abin haushi shi ne yadda ma'aikatan lafiyar wannan Asibitin suka yi ta wasa da mu kamar tamola a yayinda matata ke cikin halin rashin tabbas."
Babban abin haushi shi ne yadda Likitan ya ce dole sai mun sake yin wani gwajin baya ga cewa awoyi kadan da suka wuce mun yi wani kuma gashi masu awon a Asibitin sun tashi sai washe gari su dawo. Hakan ya tilasta mana zuwa wani wajen gwajin mai zaman kansa, a nan ma dai Maigwajin yana Asibitin Turai Yaradua yana aiki, kafin ya zo sai bayan karfe hudu. Kafin mu dawo Asibitin turai Likitan da ya tura mu gwajin ya tashi aiki wanda ya canje shi kuma ya ce bai bar masa shaidar cewa zai yi aiki wa matata ba'
A yayin zantawarmu da shi, Abubakar Masanawa ya Koka Kan yadda ma'aikatan wannan Asibitin suka rika tura majinyata a galabaice, abu mai kama da kora har sai da wata mata ta haihu a keke napep. "abin haushi tun karfe shabiyu na rana nake Asibitin ban sami kula ba amma sai ga wani Likitan misalin karfe bakwai yana fada min a baki ba takarda cewa matata ba za ta iya haihuwa a nan ba don haka sai mu garzaya da ita zuwa Asibitin Babbanruga."
Tun lokacin da naje sai misalin karfe takwas na dare ne Likitan ya ce ya ban minti talatin in sayo kayan aikin da za'a yi wa matata aiki. Da kyar na rokeshi ya ban awa daya,ina wajen sayan kayan ana kirana cewa in na wuce awa daya, ba za su yi ba sai Gobe.
'A karshe an samu fiddo da jariran a galabaice sannan babu mai kula da su sai wata ma'aikaciyar jinya wacce a zantawar mu da ita ayyuka ne suka yi mata yawa har yasa naga kazawarta a fannin kuka da jariran' Inji Abubakar Masanawa.
A karshe dukkan 'ya'yan suka rasa rayukansu ita kuma uwar ta fada cikin jinya saboda galabaita'
Masanawa ya danganta rasuwar 'ya'yansa Kan rashin tsarin aiki na hukumar Katsina State Contributory Healthcare Management Agency,rashin isassun kayan aiki da karancin ma'aikata tare da sakacin ma'aikatan lafiya,.