TATSUNIYA: Labarin Dogarawa Uku
- Katsina City News
- 22 Dec, 2024
- 34
Ga ta nan, ga ta nanku
Wasu dogarawa ne su uku, masu suna Gi, Da, da Do, suke gadin gidan Sarki. Akwai kuma wani mutum a garin mai suna Gidado.
Aikinsu
Sarki yana da kaji da yawa a gidansa. Wadannan dogarai—Gi, Da, da Do—kullum suna zuwa suna kamun fari. Idan sun kamo, sai su zuba wa kajin Sarki. Idan kajin sun ga abin farin, sai su je suna ci. Sai dogaran su kama guda uku—kowa da tasa. Daga nan sai su je su gasa, su ci.
Kullum a kofar gidan Gidado suke gasawa. Haka suka rika yi yau da gobe, har sai da Sarki ya lura cewa kajinsa suna raguwa. Sai aka soma bincike. In aka tambayi wannan, sai ya kalli wancan. Idan aka tambayi wancan, sai ya kalli wannan. Sai Sarki ya ce idan ba su fadi gaskiya ba, za a kashe su.
Akwai wani Bafulani da ke kai wa Sarki nono kullum. Lokacin da yake zuwa, yakan hadu da Gi, Da, da Do, amma ba ya iya bambanta su. Idan zai yi magana, sai ya ce: “Gidado.” Idan ya tambaye su inda za su je, sai su ce suna kan aikin Sarki.
Bayyanar Matsalar
Ranar da ake binciken bacewar kajin Sarki, sai ga Bafulatani ya iso. Da ya ji tambayoyin da ake yi, sai ya ce ya san wadanda ke cin kajin. Sai aka tambaye shi ya bayyana, sai ya ce:
"Wallahi Gidado ne yakan ci kaza kullum. Idan ina zuwa kawo nono, mukan hadu yana rike da kaza. Idan na tambaye shi inda zai kai kazan, sai ya ce Sarki ya aike shi."
Sarki ya ce a binciki gidan Gidado. Da aka je, sai aka tarar da gashin kaji ya cika kofar gidan. Wannan ya tabbatar da cewa ana amfani da kofar gidan wajen fige kajin Sarki da ake sata. Sai aka kama Gidado.
Da aka tambaye shi game da kajin, sai ya ce bai san komai ba. Sai Sarki ya ce:
“Idan ba kai ba ne, wa zai je kofar gidanka, ya yanka kaza, ya fige, ya gasa, kai kuma ba ka sani ba?”
Gidado ya nace bai san komai ba. Sai Sarki ya kasa gane gaskiyar lamari. Dogaran suka ce tun da a kofar gidansa aka ga gashin kajin, ya kamata a kashe shi.
Sarki ya amince, aka tura Gi, Da, da Do su kashe Gidado. Bayan kashe shi, sai suka kwace gidansa, suka cigaba da satar kajin Sarki ba tare da an gano su ba.
Darussa Daga Labarin
1. Kuskure ne zartar da hukunci ba tare da bincike mai kyau ba.
2. Maciyin amana, ko yaushe, zai fuskanci mummunan sakamako.
3. Azzalumin Sarki ba zai iya zalunci ba sai da taimakon bafade.
4. Wata shari’ar sai a lahira ake samun gaskiyarta.