KIWON LAFIYA: Cutar da Tafi Yaduwa a Lokacin Sanyi, Hanyoyin Kamuwa da Yadda Za a Iya Kare Kai daga Kamuwa da Ita
- Katsina City News
- 20 Dec, 2024
- 77
Katsina Times
A lokacin sanyi, cututtuka masu yaduwa na kara kamari sakamakon canjin yanayi da kuma yadda jama’a ke zama kusa da juna a cikin wurare marasa isasshen iska. Wasu daga cikin cututtukan da suka fi yaduwa a wannan lokaci sune: Ciwon mura (common cold), da kuma wasu cututtukan numfashi, ciki har da Ciwon huhu (pneumonia), da ciwon kai da makogwaro (flu da sore throat).
Hanyoyin Kamuwa da Cutar
1. Ta iska: Yawanci, cututtukan numfashi na yaduwa ta hanyar iska mai dauke da kwayoyin cutar da wani mai cutar ya tofa, Tsiftarwa, ko yin tari.
2. Ta taba abubuwa: Kwayoyin cuta na iya rayuwa a saman abubuwa kamar kofuna, murfin kofa, ko tebur na tsawon lokaci. Idan aka taba irin wadannan wurare sannan aka shafi hanci ko baki, mutum na iya kamuwa.
3. Kusa da mai cutar: Kusa-kusa da masu ciwon mura ko tari, musamman a cikin gidaje ko wuraren da jama’a ke taruwa kamar makarantu da ofisoshi, yana kara yiwuwar kamuwa da cutar.
Alamomin Cututtukan da Suke Yaduwa a Lokacin Sanyi
- Tari da mura
- Saurin gajiya
- Matsanancin ciwon kai
- Ciwon makogwaro
- Zazzaɓi
- Shanyewar murya
Hanyoyin Kare Kai daga Kamuwa
1. Tsafta: Wanke hannuwa da sabulu akai-akai, musamman bayan shiga waje ko kafin cin abinci.
2. Nesa da masu cutar: Gujewa kusantar mutane da ke fama da mura ko tari.
3. Sanya rigar sanyi: Sanya tufafi masu dumi don kare jiki daga matsanancin sanyi.
4. Rufe baki da hannu: Idan mutum zai yi tari ko atishawa, ya rufe bakinsa da hannu ko tissue don rage yaduwar kwayoyin cutar.
5. Shan ruwa mai yawa: Shan ruwa yana taimakawa wajen kiyaye lafiyar jiki da numfashi.
6. Taimakon ganyen: Shan ganye kamar na shayi mai zafi da zuma na rage alamomin mura.
Lokacin Neman Magani
Idan mutum ya fuskanci cutar da ta dauki tsawon lokaci ko kuma zazzaɓi mai tsanani da ke tare da rashin numfashi, ya kamata ya garzaya asibiti don samun kulawar kwararru.
Lokacin sanyi yana bukatar taka tsantsan wajen kula da lafiya don gujewa kamuwa da cututtuka masu yaduwa. Wajibi ne mutane su yi taka tsantsan wajen tsafta da kuma amfani da hanyoyin kariya don kiyaye lafiyarsu.