Musa Gafai Ya Sauya Sheka Zuwa APC Saboda Nasarorin Gwamna Dikko Radda
- Katsina City News
- 19 Dec, 2024
- 117
Jagoran matasa kuma fitaccen ɗan kasuwa, Honarabul Musa Yusuf Gafai, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC, yana mai bayyana cewa nasarorin da Gwamna Malam Dikko Umar Radda ke cimmawa sun zama abin burgewa da girmamawa.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Hon. Musa Yusuf Gafai, wanda ya yi takarar kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar Katsina ta Tsakiya a zaɓen baya, ya bayyana cewa ya yanke shawarar shiga APC domin mara baya ga gwamna Dikko Radda wajen ci gaba da ayyukan gina jihar Katsina.
"Na yanke shawarar ficewa daga PDP zuwa APC ne saboda yadda Gwamna Malam Dikko Radda ya tsayu wajen inganta tsaro, bunkasa ilimi, da gina sabuwar Katsina. Ayyukansa sun kai ga ƙananan garuruwa, suna canza rayuwar mutane," in ji Hon. Musa Gafai.
Ya ƙara da cewa, tun lokacin da aka kafa gwamnatin Dikko Radda, jihar Katsina ta fara samun ci gaba a fannoni daban-daban, wanda hakan ya sa ya ji ya dace ya dawo gida domin bayar da gudummawarsa ga ci gaban jihar.
Hon. Musa Yusuf Gafai, wanda ya kasance shugaban matasa da daraktan tuntuba na kwamitin yakin neman zaben PDP a baya, ya bayyana cewa, “Ina alfahari da yadda Gwamna Dikko Radda ya ke tafiyar da lamurran jihar Katsina. Tabbas, ina da yakinin za mu kai jihar Katsina a mataki mai alfanu, wanda za a yi koyi da shi a Najeriya."
Hon. Musa Gafai ya kuma tunatar da cewa, yana daga cikin jagororin da suka fara tallata Dikko Radda tun farkon tafiyarsa, inda ya kafa ƙungiyar “Katsina Ta Dikko” domin mara masa baya. Yanzu kuma, ya ce, dawowarsa jam’iyyar APC tamkar dawowa gida ne gareshi.
Ficewar Hon. Musa Gafai daga PDP zuwa APC na nuni da yadda ayyukan gwamnatin Dikko Radda ke jan hankalin mutane, musamman matasa da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa a jihar Katsina. Wannan sauyin ya sake tabbatar da karfin jam’iyyar APC a jihar da kuma burin ta na ci gaba da jagorancin Katsina.