Mutanen jihar Katsina na kokarin kiyaye dokokin KASSROTA. - Shugaban Hukumar KASSROTA Katsina.
- Katsina City News
- 19 Dec, 2024
- 262
Shugaban hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa na jihar Katsina, KASSROTA, Major Garba Yahaya Rimi mai ritaya, ya yaba wa al'ummar jihar Katsina musamman masu ababen hawa bisa ga yadda a yanzu suke kiyaye dokar tuki a jihar.
Shugaban hukumar ya yi wannan yabon ne a yayin wata fira ta musamman da Jaridar KatsinaTimes a ranar Larabar nan.
Ya ce, da farko hukumar tata kai ruwa rana da al'umma kan kiyaye dokokin Tuki a matakin jiha da na Kasa, amma yanzu sun fara kiyaye dokokin bakin gwalgwaldo.
"Lokacin da muka zo hukumar nan, yawancin mutane ba sa bin dokokin da aka tsara na hanyoyinmu wanda zai kare ransu da dukiyarsu da lafiyarsu. An fito da wadannan dokokin ne saboda a kare rayuka, lafiya da kuma dukiyoyin al'ummar jihar katsina da masu zowa su ratsa jihar su tafi wasu jihohi." In ji shi.
Ya ce amma yanzu da al'umma suka ga alfanun dokokin, suna kiyaye wa, har ma suna samun rahotannin cewar a wasu wurare al'umma da kansu ke wa mutanen da aje kaya ko kasa kaya sana'a bisa hanya magana a kan su dauke su.
Ya kara da cewa, yanzu ta kai ma su al'umma da kansu ke gayyato jami'an hukumar da su zo su tabbar da masu ababen hawa suna kiyaye dokokin hanya a lokacin da aka bude wata sabuwar hanya ko aka gyara ta.
DG Garba Rimi, ya ba wa masu ababen hawa a jihar tabbacin cewar, hukuma ko gwamnati ba za ta zo da wani abu da zai cutar da su ko wulakanta su ba, face abin da zai inganta rayuwarsu da zamantakewarsu musamman al'amarin hanya wanda kowa ke da hakki bin ta.
"Ba muna so mu tursasa wa mutane ba, amma muna so su yi amfani da hankalinsu da kuma yadda doka take saboda tsaron lafiyarsu."
"Abin da muke roko ga mutanen jihar katsina baki daya masu amfani da ababen hawa da wanda ba su yin amfani da su; a yi kokari a kiyaye dokokin da aka tsara na hanya. Matukar aka kiyaye dokaki, ba za a samu matsaloli ba." Ya tabbatar.