Hukumar EFCC Ta Fara Binciken Karkatar da Tankunan Karfe na Ruwa a Karamar Hukumar Kurfi
- Katsina City News
- 17 Dec, 2024
- 524
Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta fara bincike kan zargin karkatar da tankunan karfe masu samar da ruwan sha a Karamar Hukumar Kurfi, Jihar Katsina. Wannan binciken ya biyo bayan korafi da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam, Network for Justice, ta shigar a ranar 17 ga Satumba, 2024. Shugabannin ƙungiyar da suka shigar da korafin sun haɗa da Abdullahi Hassan Kofar Sauri, Dokta Bashir U. Kurfi, da Wing Commander Gambo Kurfi (rtd).
Zarge-Zargen da Aka Gabatar
Korafin ya bayyana cewa wasu shugabanni a karamar hukumar sun haɗa baki wajen rusa babban tankin ruwan ƙarfe da ke samar da ruwa ga al’umma, suka siyar da sassan kayan tankin tare da azurta kansu da kuɗin.
An kuma zargi cewa wasu daga cikin kayan tankin da aka kwashe sun ɓace, yayin da wasu aka siyar da su ba bisa ka’ida ba. Wasu daga cikin kayan da suka rage an kai su ofishin ‘yan banga don ajiya, amma daga bisani sabon DPO na Kurfi, Ilyasu Mohammed Maradi, ya umarci a mayar da su wani wuri daban, wanda aka ce daga baya aka ci gaba da siyar da kayan a ɓoye.
Haka nan, kayan da aka ajiye a Makarantar Firamare ta Maimani da waɗanda aka tono daga rijiya, suma an yi zargin sun ɓace.
Takardar Korafin ta bayyana sunayen waɗanda ake zargi da hannu a lamarin:
Aminu Maradi, Magajin Garin Kurfi, Ilyasu Mohammed Maradi, DPO na Kurfi, Mustapha Sani, Dillalin ƙarfe, Dayyabu Abba (D-Naste), Mai aikin ƙarfe, Usman Sani da Mannir Gambo, ‘yan ƙaramar hukuma
Lamarin ya haifar da damuwa ga al’ummar Kurfi, waɗanda yanzu haka ke cikin ƙunci saboda ƙarancin ruwa. Mafi yawan su sun koma amfani da ruwan tafki, wanda ke haifar da barazana ga lafiyarsu.
Da yake martani kan zarge-zargen, Shugaban Karamar Hukumar Kurfi, Dakta Mannir Shehu Wurma, ya musanta cewa yana da hannu a lamarin. Ya bayyana cewa tankin ya lalace tun kafin ya hau mulki.
"Abin da na tarar kenan lokacin da na hau mulki. Tankin ya lalace kuma wasu daga cikin jama’a har da wata ƙungiyar addini sun nemi a ba su ƙarfen tankin, amma na ki amincewa saboda aikin gwamnatin tarayya ne, ba na karamar hukuma ba," inji shi.
Ya kuma ƙara da cewa, "Daga baya ne na ji labarin cewa an fara rusa tankin ba tare da sanina ba. Wasu dattawa da ‘yan banga sun yi zaman tattaunawa suka cimma matsaya cewa a siyar da wasu sassan tankin domin samun kuɗin tsaro. Amma ban san wannan tsari ba, kuma ban halarci zaman ba."
Malam Dayyabu, shugaban ‘yan banga na Kurfi, ya tabbatar da cewa an siyar da ƙarfen tankin a kan kuɗi ₦270,000. Ya ce daga cikin kuɗin, ₦100,000 aka ba wa ‘yan banga don kula da tsaro, ₦50,000 aka bai wa mai lura da kayan, sannan ₦40,000 aka ware wa ofishin ‘yan banga.
Tawagar EFCC, tare da wakilan ƙungiyar Network for Justice da jaridar Katsina Times, sun ziyarci wurare uku da abin ya shafa. A wajen da aka kafa tankin a Unguwar Bayan Dam, babu wani abu da ya rage sai alamun tsohon tankin. Sassan kayan da suka rage an same su a ofishin ‘yan sanda, yayin da sauran kayan suka ɓace.
Al’ummar Kurfi sun nuna damuwarsu kan halin da suka shiga na rashin ruwa mai tsafta, suna kira ga hukumomi da su dauki matakin gaggawa don magance matsalar.
Shugaban na ƙaramar hukumar Kurfi Dokta Mannir Wurma ya sha Alwashin gyara da maida Tankin kamar yadda yake a baya domin amfanin al'ummar karamar hukumar ta Kurfi.
Saidai hukumar EFCC ta sha alwashi tare da gano hakikanin masu hannu a wannan al'amari don fuskantar shari'a