Gwamnan Jihar Katsina Ya Rantsar Da Sabon Shugaban Ma'aikatan gidan Gwamnati.

top-news

Auwal Isah Musa, Katsina Times 


Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda Ph.d, ya rantsar da Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar.

Bikin rantsarwar an gudanar da shi a zauren majalisar jihar, a lokaci guda tare da rantsar da wasu masu bada shawar ta musamman guda uku da suka hada da: Alhaji Mustapha Bala Batsari a matsayin mai bada shawara kan habaka Kasuwanci, Alhaji Ahmed Nasiru Sada mai bada shawara kan raya Karkara da da Zamantakewar Al'umma, da kuma Hajiya Bilkisu Suleiman Ibrahim a matsayin mai bada shawara kan Banki da harkar Kudi.

Har wayau duk a wajen taron rantsarwar, an kuma karrama tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar, Honorabul Jabiru Abdullahi Tsauri, wanda aka nada a matsayin mai kula da sabuwar Hukumar Kawance Don ci Gaban Afirka na kasa (NEPAD). 

Da yake jawabi jin kadan bayan rantsarwar, gwamna Radda, ya bukaci wadanda aka rantsar da su shirya shirin bullo da duk wasu tsare-tsare na gina al'umma don samar mata dankyakkyawar makoma.

Gwamna Radda har wayau, ya kuma bukaci sabbin shugabannin da aka rantsar da su fito da dabarun gina nagartacciyar makomar al'ummar jihar, da kuma samar masu da ingantaccen shugabanci na gari. 

Sabon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin, Alhaji Abdulkadir, tsohon danmajalisar wakilai ne a shekarar 2007 zuwa 2011, kuma tsohon mai ba tsohon gwamnan jihar, Masarai, shawara kan noman rani ne, kuma tsohon mai ba da shawara na musamman kan karfafawa da kuma shugabacin hukumar kudaden Naira Biliyan 2 daga CBN MSMDEDF da SPV na jihar katsina, sannan ya rike mukamin Manajan Darakta a Hukumar Samar da Ruwa ta Jihar wanda ya kawo shi zuwa mukaminsa na shugaban ma'aikatar fadar gwamnatin jihar a yanzu.

An bayyana Alhaji Abdulkadir a matsayin gogaggen ma’aikacin gwamnati wanda ya kawo kyakkyawan tsarin ci gaba da hidimtawa al'ummar jihar, tare da taka muhimmiyar rawa a tarihin daukacin mukaman da ya rike.