SERAP Ta maka Tinubu a kotu kan gaza bincikar Naira Biliyan 57 da su ka bace a Ma’aikatar Jin Kai
- Katsina City News
- 15 Dec, 2024
- 78
Kungiyar Kare Hakkokin Zamantakewa da Tattalin Arziki (SERAP) ta shigar da kara a gaban kotu kan Shugaba Bola Tinubu da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Mr. Lateef Fagbemi (SAN).
Karar dai na da alaka da gazawarsu na yin aiki tare da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa don bincikar zargin bacewar sama da naira biliyan 57 na kudaden jama’a daga Ma’aikatar Jin Kai da Rage Talauci ta Tarayya a shekarar 2021.
SERAP ta bayyana cewa zarge-zargen sun fito ne a cikin rahoton kididdiga na 2021 da Ofishin Mai Binciken Kudaden Gwamnati na Tarayya ya fitar a watan Nuwamba 2024.
SERAP ta bayyana a ranar Lahadi cewa karar da ta shigar ranar Juma’a a Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Legas, mai lamba: FHC/L/MISC/876/2024, ta ambaci Fagbemi a matsayin wanda ake kara, tana neman kotun ta tilasta wa Shugaba Tinubu ya umarci Fagbemi ya hada kai da hukumomin yaki da cin hanci don bincikar zarge-zargen cikin gaggawa.
Haka kuma SERAP tana neman kotun ta tabbatar da cewa wadanda suka dace da alhakin bacewar naira biliyan 57 an gurfanar da su a kotu, idan an sami isassun shaidu, tare da dawo da dukiyar da aka gano zuwa baitul malin gwamnati.
Culled from Daily Nigeria