TARIHIN UNGUWAR TURAWA TA KATSINA ( GRA).
- Katsina City News
- 15 Dec, 2024
- 150
Unguwar Turawa ko Kuma GRA, ta Katsina ta samo asalintane a lokacin da Turawan Mulkin Mallaka suka zo Katsina acikin shekarar 1903. Turawan Ingila sune zo Katsina alokacin mulkin Sarkin Katsina Abubakar(1887-1905). Bayan anyi yarjejeniya da Turawan, Wanda ya nuna cewa Kasar Katsina kamar sauran Kasashen Daular Usmaniyya sun Mika wuya ga Turawa, akan mulkin Mallaka.
Dalilin kafa Unguwar GRA, shine tsarin da Turawan suka kawo na ( Indirect Rule) watau zasu mulki mutane amma ta hanyar Sarakunan su na Gargajiya. A sabili da hakane sai suka ware kansu suka kafa Unguwarsu ta daban a wajen Gari, da farko sun Fara Kiran Unguwar da suna "White reserved Area" daga baya ta koma GRA watau Government Reserved Area. Turawan Mulkin Mallaka sun ba Sarki Sandar Girma, sannan suka sake nadashi. Turawan Mulkin Mallaka basu amince subar Sarki da nadinsa ba, saboda haka sai suka bullo da ba Sarki Sandar Girma, don ya tabbatar cewa akwai na gaba dashi watau Rasdan, da D. O, da Gwamna da sauransu, Kuma Yana karbar umarni daga garesu, wannan shine mulkin ( indirect Rule) watau a mulki mutane ta hanyar Sarakunan su.
A Unguwar GRA dinne aka Gina Gidan Rasdan, Wanda daga baya gidanne ya koma Tsohon Gidan Gwamnatin Jihar Katsina. Akwai kuma Tsohon Ofishin Lardi na Katsina inda a yanzu nan ne Ofishin Maaikatar kula da kananan Hukumomi da Sarautu ta Jihar Katsina. Akwai Tsohon Masaukin Baki na Jihar Katsina Wanda ada ake Kira da suna " Catering Rest House". a yanzu ake kiran wurin da suna Katsina Motel. Dukkan wadannan wuraren an ginasune a zamanin Mulkin Mallaka. Haka kuma a Unguwar GRA akwai Makaranta Firamare ta Modoji wadda asalinta Makarantar Mishan ce ta farko a Katsina da ake Kira da suna " St. John Primary School". Daga baya ne Gwamnatin Jihar Arewa ta Tsakiya ta amsheta ta canza mata suna zuwa Modoji Primary School ta Kuma mayar da ita Makarantar Gwamnati.
A Unguwar Barikine ko GRA, duk shekara Sarkin Katsina yake Shirya Hawan Bariki. Idan anyi Hawan Sallah, rana ta biyu Kuma sai Sarki ya hau da mutanen shi aje Bariki, a gaida Rasdan, sannan a zauna a tattauna al' ummar Gwamnati a lokacin. Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (1906-1944) shine Sarki na farko daya Fara wannan Hawa na Bariki, acikin shekarar 1907, Kuma Rasdan na farko da aka Fara yima Hawan Bariki shine H. R. Palmer.
Alh. Musa Gambo Kofar soro.