TARIHIN HARUNA UJI (KASHI NA DAYA)

top-news

Alhaji Haruna Uji Hadejia
An haifi Alhaji Haruna Uji a Unguwar Gandun Sarki, cikin garin Hadejia, a shekarar 1946. Mahaifinsa, Mallam Ibrahim, malami ne kuma limamin Gandun Sarki, yayin da mahaifiyarsa, Zainabu, itama mutumiyar wannan unguwa ce. A nan ne Haruna Uji ya taso ya kuma girma cikin ilimi da tarbiyya.  

Tun yana shekara shida, mahaifinsa ya sanya shi a makarantar Allo da ke kofar gidansu, karkashin kulawar wani malami mai suna Mallam Alhaji. Haruna ya shafe shekaru uku yana koyon karatun Allo a Gandun Sarki, sannan suka koma garin Birniwa tare da malaminsa, mai nisan kilomita 45 daga Hadejia. A Birniwa, Haruna ya kara samun ilimi mai yawa tare da sauran almajirai.  

Bayan wasu shekaru biyu, suka dawo Hadejia inda suka ci gaba da karatu a Gandun Sarki. Haruna Uji ya samu karin ilimi fiye da sauran yara na lokacin, musamman saboda jarumtarsa wajen bin malamai neman ilimi. Ya bar makarantar Allo yana dan shekara goma sha biyu, bayan ya kammala karatu mai zurfi.  

Asalin Inkiyar Haruna Uji
Sunansa na yanka shi ne Haruna, wanda ya ci sunan wansa, Mallam Haruna. Inkiyar "Uji" kuwa ta samo asali ne daga lokacin da matan kanin babansa suke kiransa da "Mijin Iya Kura." Yaran unguwarsu kuwa, saboda rashin iya furta kalmomi da kyau, suna ce masa "Ujin Iya Kura," wanda daga bisani ya rage zuwa "Uji."  

Siffar Haruna Uji
Haruna Uji mutum ne baki, mai matsakaicin tsawo da jiki, yana da farin hakora da bakin gashi. Yana yawan barin gashin baki, kuma yana da murya mai dadi da kauri kadan. Haruna mutum ne gwanin ado, musamman a cikin manyan kaya na sarauta, kuma yana saka 'yar shara a lokacin zafi.  

Haruna Uji mutum ne mai fara’a, nagarta, da kyauta. Yana da dabi’ar taimako, sannan bai da wata nakasa a fili.  

Sana’o’in Haruna Uji

Farauta da Noma
Bayan ya kammala makarantar Allo, Haruna ya fara farauta, wanda ita ce sana’arsa ta farko. Wannan sana’a ta koya masa jarunta da rashin tsoro. Haka kuma, ta sanya ya koyi dabaru da lakani na tsare kai.  

Daga bisani, ya shiga aikin noma tare da mahaifinsa, inda ya samu kwarewa sosai har ya rika noma gonarsa.  

Tukin Mota
Haruna Uji ya fara aikin tukin mota ta hanyar zama yaron mota ga wani mai suna Jibrin Dan Amingo, wanda dan asalin Danbatta ne a Jihar Kano. Wannan aiki ya bashi damar fita daga Hadejia zuwa Kano da wasu garuruwa na Arewacin Najeriya.  

Sana’ar Waka
Wakar Gurmi ce ta shahara wajen Haruna Uji, amma bai gaji waka daga iyalinsa ba, domin mahaifinsa malami ne. Ya fara sha’awar Gurmi ne a wajen wani ma’aikacin titi mai suna Dan-Mato, wanda suke aiki tare a hanyar Mallam Madori zuwa Gumel. Duk lokacin da Dan-Mato ke kada Gurmi a lokacin hutu, Haruna yakan yi kallon tsanaki har abin ya shiga ransa.  

A gida, Haruna yakan hada gurmi daga gwangwani da tsirkiya, yana kwaikwayon Dan-Mato har ya koya kada gurmi da kansa. Bayan haka, ya ci gaba da kara inganta fasaharsa, yana waka a bukukuwa da taruka, musamman na samari da 'yan mata.  

Daga bisani, Haruna ya bar sana’ar tukin mota ya koma sana’ar kidan gurmi gaba daya.  

Haruna Uji A Hadejia
Haruna Uji ya shahara a garuruwa daban-daban na Arewacin Najeriya saboda wakokinsa na Gurmi. Wannan sana’a ta bashi damar kasancewa wani jigo a al’ummar sa, tare da samar da nishadi da al’adu.  

Rubutawa: Muhammad Aji Hadejia  
Tushen Labarin: Hadejia A Yau! Rubutawa Hadejiawa