Gwamnatin Tinubu na amfani da kuɗaɗen tallafin mai don cigaban al’umma, inji Ministan Yaɗa Labarai
- Katsina City News
- 13 Dec, 2024
- 211
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa ana amfani da kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin man fetur wajen aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa ƙarƙashin Shirin Sabunta Fata na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Idris ya bayyana haka ne a Taron Shekara-shekara na Cibiyar Harkokin Jarida ta Duniya (IPI) na 2024 da aka gudanar a Abuja, wanda ke ɗauke da taken "Dimokiraɗiyya, 'Yancin Kafofin Watsa Labarai, da Muhimmancin Kare Sararin Jama'a na Nijeriya."
A cewar sa, ana amfani da kuɗaɗen tallafin da aka ajiye wajen shirye-shiryen da suka haɗa da bashin ɗalibai, gina ababen more rayuwa, bashi mai rahusa ga jama’a, bunƙasa aikin gona, da kuma shirin jinƙai na musamman.
Ya ce gwamnatin na mayar da hankali kan cigaban al’umma ta hanyar sauye-sauyen tattalin arziki da zuba jari domin samun cigaba mai ɗorewa ga al’ummar Nijeriya.
Ya ce: “Ana karkatar da tiriliyoyin Naira da aka rasa wajen shirye-shiryen tallafi marasa amfani zuwa manyan ajiyoyi, wanda hakan ke bai wa gwamnati damar saka jari a muhimman fannonin tattalin arziki."
Ministan ya bayyana cewa gwamnatin na gudanar da sauye-sauyen tattalin arziki da suka shafi bunƙasa fannonin tattalin arziki, raya ƙwarewar ɗan'adam, da samar da cigaban tattalin arziki mai inganta kowa.
Ya ce babban abu a cikin waɗannan sauye-sauyen shi ne shirin haraji da aka gabatar wanda zai sauƙaƙa biyan haraji tare da rage wa talakawa nauyi.
“Ɗaya daga cikin abubuwan da suka ja hankali a wannan gyara shi ne sababbin kariya daga haraji da za su amfani mutane da kamfanoni da dama.”
Ya yi nuni da cewa waɗannan sauye-sauyen sun dace da manyan dabarun tattalin arziki, da tabbatar da samun dauwamammen sauyi da samar da Nijeriya mai gasa a duniya.
Idris ya kuma yi magana game da mayar da hankali na gwamnatin kan canjin makamashi, yana bayyana shi a matsayin muhimmin ɓangare na shirin cigaban Nijeriya.
Ya ce, “Shugaba Tinubu na jagorantar Nijeriya cikin wani sabon mataki na canjin makamashi, inda ya ƙaddamar da shirin shugaban ƙasa na canza ƙasar daga amfani da man fetur zuwa iskar gas ɗin da ake kira Compressed Natural Gas (CNG) a matsayin man motoci da injina.”
Wannan sauyi, inji shi, yana rage farashin sufuri zuwa kashi 60, da samar da ayyukan yi, da jawo jari mai yawa.
Game da kafofin watsa labarai, Idris ya tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu tana ba da muhimmanci wajen kare ’yancin kafofin watsa labarai da sararin jama’a.
Ya ce: "Tun lokacin da Shugaba Tinubu ya hau kan karagar mulki a watan Mayu 2023, mun sake jaddada aniyar mu ta tabbatarwa da faɗaɗa 'yancin 'yan jaridun Nijeriya."
Sai dai, ya ja hankali cewa ’yanci ba shi da amfani idan babu sanin haƙƙi. Ya ce kafofin watsa labarai su kasance masu gudanar da muhawara mai amfani da kuma kula da hukumomi su ɗauki alhakin ayyukan su ba tare da tsananta wa masu ra’ayi mabambanta ba.
Idris ya ce: “Kowane ’yanci yana tare da sanin haƙƙi; ’yanci ba shi da ma’ana idan babu iyaka."
Ya kuma bayyana cewa Shugaba Tinubu yana ba da fifiko wajen gyaran tsarin shari’a domin tabbatar da kare haƙƙoƙin ɗan'adam, ciki har da ’yancin faɗar albarkacin baki da haɗin kai.
Ya bayyana gyaran a matsayin ginshiƙi wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya da tabbatar da bin doka a Nijeriya.
A ƙarshe, Idris ya ce matakan da gwamnati ke ɗauka suna da matuƙar muhimmanci wajen gina Nijeriya mai arziki, inda ’yancin kafofin watsa labarai da alhakin 'yan ƙasa ke taka muhimmiyar rawa wajen tsara tafiyar dimokiraɗiyya ta ƙasar.
Culled from Almizan Hausa