Gwamna Radda Na Katsina Ya Lashe Kyautar Jagoran Tsaro Mafi Gamsuwa a Afirka ta Yamma
- Katsina City News
- 12 Dec, 2024
- 195
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Jihar Katsina ta samu babban karramawa a matakin kasa da kasa kan kokarin da take yi wajen magance matsalar tsaro, inda aka bai wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, kyautar "Gwamna Mafi Gamsuwa da Kishin Tsaro a Afirka ta Yamma da ta Tsakiya." An gabatar da wannan kyauta ne a taron shekara-shekara na "18th Africa Security Watch Conference" da ake gudanarwa a birnin Doha, kasar Qatar.
Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Hon. Faruk Lawal Jobe, ne ya wakilci Gwamna Radda wajen karbar kyautar, wadda ke nuna gamsuwa da jajircewarsa wajen tabbatar da tsaro a jihar da kewaye.
Babban Hafsan Sojojin Ruwa na Najeriya (Chief of Naval Staff), Admiral Awwal Zubairu Gambo, ya gabatar da kyautar ga gwamnan. Ya bayyana cewa an bai wa gwamnan wannan karramawa ne saboda irin nasarorin da ya samu wajen inganta zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.
Taron Africa Security Watch Conference ya tattaro manyan masu ruwa da tsaki, kwararru a sha’anin tsaro, da shugabanni daga sassa daban-daban na duniya domin tattauna hanyoyin magance kalubalen tsaro da ake fuskanta a Afirka.
Karramawar da aka yi wa Gwamna Radda na nuna yadda jihar Katsina ke daukar matakai na musamman wajen yakar matsalolin tsaro tare da bunkasa ci gaban tattalin arziki. Tuni aka yaba da manufofin gwamnan na samar da zaman lafiya mai dorewa da inganta rayuwar al’umma.
Wannan kyauta ta zama wata alama ta yabo da kuma kara karfafa gwiwa ga Gwamna Radda da sauran shugabanni wajen fuskantar matsalolin tsaro da sabbin dabaru.