Gamayyar Kungiyar Goyon Bayan APC Ta Bukaci Musa Gafai Ya Hada Kai da Gwamnatin Dikko Radda

top-news

Kwamared Shehu Kofar Soro

A yau, Gamayyar Kungiyoyi Goyon Bayan Jam’iyyar APC a karkashin jagorancin Kwamared Shehu Kofar soro ta taru tare da yin kira ga Hon. Musa Yusuf Gafai da ya shiga cikin jam'iyyar APC a karkashin jagorancin nagartaccen mulkin Gwamna Dikko Umar Radda na Jihar Katsina.  

Kwamared Shehu Kofar soro ya bayyana cewa Hon. Musa Yusuf Gafai na daga cikin wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen nasarar gwamnatin APC a jihar, inda ya kasance daya daga cikin tsofaffin jagororin da suka assasa wannan gwamnatin. Ya kuma bayyana cewa Gafai ya yi fice a matsayin jagoran ƙungiyar "Katsina Ta Dikko Ce", wadda ta mara wa Gwamna Radda baya tun daga lokacin yakin neman zabe.  

Kungiyar ta bayyana cewa shigar Gafai cikin wannan gwamnati zai kara karfafa hadin kai da kuma bunkasa ci gaba da nagartar mulki a Jihar Katsina.  

Mambobin kungiyar sun bayyana fatan cewa kwarewa da shugabancin Gafai zai taimaka wajen cimma manufofin Gwamna Radda na kawo ci gaba mai dorewa a jihar. Sannan sun bukace shi da ya amince da wannan dama don cigaba da hidimtawa al’ummar Jihar Katsina.