A wani yunkuri na tabbatar da cewa ba a sami wata tangarda a aikin Hajjin bana ba,
Babban bankin Najeriya ya amince da bai wa hukumar aikin Hajji ta Kasa tsurar kudaden guzirin Alhazai don a raba musu a hannu.
Wannan ya biyo bayan tsoma bakin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya yi kamun ƙafa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a madadin maniyyatan
Tun da farko, babban bankin na Najeriya ya fito da wani tsari na tanadar wa kowane Alhaji katin hada-hadar kudi don sauƙaƙa harkokin cinikayya ga maniyyatan a ƙasa Mai tsarki, sai dai hakan ka iya zama ƙalubale musamman ga maniyyatan Najeriya da ke fitowa daga karkara wadanda suka fi sabawa da hada-hadar kuɗi-hannu, wannan ne ya sanya Shugaban kasar ya bai wa Babban Bankin umarnin hanzarta komawa amfani da tsarin bayar da guziri na tsaba ga maniyyatan, umarnin da tuni babban bankin ya fara aiki da shi
Tuni dai Hukumar aikin Hajji ta ƙasa NAHCON ta yi maraba da wannan mataki, inda ta bayyana shi a matsayin wata babban nasara ga yunkurinta na samar da walwala ga Alhazai
"Amincewar da CBN ta yi da komawa tsarin hada-hadar kudin tsaba, wani abin farin ciki ne ga alhazan Najeriya, wadanda a yanzu za su iya gudanar da aikin Hajjinsu cikin sauki" inji hukumar
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ganawarsa da Mataimakin Shugaban ƙasa, Kwamishinan Kudi na NAHCON, Aliu Abdulrazaq, ya tabbatar da cewa, “Wannan nasarar ta biyo bayan shiga tsakani da mataimakin Shugaban kasa yayi ne inda ya gayyaci mataimakin gwamnan babban bankin kasar tare da rokon bankin da su yi watsi da batun bai wa maniyyatan katin kuɗin a aikin hajjin 2025, wannan babbar nasara ce ga NAHCON.
“Idan ka je Saudiyya, galibin wuraren da mahajjata ke gudanar da ibadarsu, za ka ga na'urar cire ķuɗi mai sarrafa kants guda daya ce, hakan na haifar da cunkoso da ɓata lokacin ibada, yana da matukar wahala ga mahajjata su iya sayen duk abin da suke so su saya.
“Na biyu, kashi 95 cikin 100 na alhazan Najeriya manoma ne da makiyaya da ba su saba da hada-hadar kuɗin kati ba, kai har tsaba wasunsu kan sami matsala wajen tantance canji"
“Amma daga yanzu muna da kwarin gwiwa cewa aikin Hajji ba zai zo da cikas ba, dama shirye-shirye sun yi nisa sosai, matsalar tsabar kudi ce ta rage mana kuma a yau, an magance mana ita.”
Ana sa ran ɗaukan wannan matakin zai bai wa alhazan Najeriya damar mayar da hankali kan ayyukansu na ibada ba tare da sun yi fama da matsalolin kuɗi ba
Stanley Nkwocha
Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai da Sadarwa
(Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa)
24 ga Afrilu, 2025