Dan Majalisar Wakilai Ya Rabawa 'Yan Midiya Na'urar Kwamfuta 51, Ya Kuma Kaddamar Da Muhimman Ayyukan Raya Kasa
- Katsina City News
- 11 Dec, 2024
- 42
Dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Dutsinma da Kurfi, Alhaji Balele Dan’arewa, ya gudanar da wani muhimmin aikin tallafi ga al’umma, inda ya raba wa ‘yan Midiya na mazabarsa na’urori masu kwakwalwa (computers) guda 51 tare da tallafin kudi naira dubu ɗari ga kowannensu. Wannan mataki na daga cikin kokarinsa na tallafawa ayyukan sadarwa da kuma bunkasa harkokin aikin 'yan midiyar a yankin.
A yayin wannan bikin rabon kayayyakin, wanda ya gudana ranar Asabar, 7 ga watan Disamba, a Kurfi, Alhaji Balele Dan’arewa ya kuma kaddamar da wasu muhimman ayyukan raya kasa da suka haɗa da kafa fitilu masu amfani da hasken rana (solar lights) a yankuna daban-daban na mazabar. Wannan ya zo ne domin kawo karshen matsalar rashin haske da kuma inganta tsaron al’umma.
Alhaji Aminu Balele ya bayyana cewa wannan mataki wani bangare ne na kyautata rayuwar jama’a, tare da mayar da hankali kan muhimman ayyuka da za su bunkasa lafiya, tsaro, da jin dadin al’umma. Ya ce: “Wannan ba shi ne aikin farko ba, kuma ba zai zama na ƙarshe ba. Akwai shirye-shiryen ayyukan raya kasa masu tarin yawa da za mu aiwatar a mazabun Dutsinma da Kurfi.”
A yayin taron, wanda ya samu halartar ‘yan siyasa, wakilan al’umma, malamai, da sauran masu ruwa da tsaki, Alhaji Aminu Balele ya yi kira ga al’ummar yankin da su ci gaba da ba shi hadin kai domin tabbatar da ci gaban yankin. Ya ce cigaba ba ya tasiri sai an samu haɗin kai daga dukkanin bangarorin al’umma.
Mahalarta taron sun yaba da wannan kokari na dan majalisar, inda suka bayyana cewa irin wannan aikin shi ne ginshikin kyakkyawan shugabanci, tare da fatan cewa zai ci gaba da samar da ayyuka masu amfani da zasu karfafa cigaban al'umma.
Wannan ya tabbatar da cewa Dan majalisar yana mayar da hankali kan bukatun jama’arsa, ba wai kawai a fannin ilimi ba, har ma a bangarorin tsaro, lafiya, da walwala, wanda hakan ya zamo abin koyi ga sauran shugabanni.