Gwamnatin Jihar Katsina Ta Kafa Kwamitoci Biyu Don Kula Da Kayayyakin Gwamnati Da Na Al’umma, Da Sulhu Tsakanin Manoma Da Makiyaya
- Katsina City News
- 10 Dec, 2024
- 91
Daga Muhammad Ali Hafizy (Katsina Times)
A ranar Talata, 10 ga Disamba, 2024, gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Radda ta kaddamar da kafa kwamitoci guda biyu domin kula da kayayyakin gwamnati da na al’umma, da kuma samar da sulhu tsakanin manoma da makiyaya.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Garba Faskari, shi ne ya jagoranci taron kaddamarwar. Kwamitocin sun kunshi wakilan bangarori daban-daban ciki har da Sakataren Gwamnati, Magajin Garin Katsina, Magajin Garin Daura, Hukumar ’Yan Sanda, da Hukumar Hisbah, tare da wasu hukumomi masu ruwa da tsaki.
A jawabinsa, Faskari ya bayyana muhimmancin kula da kayayyakin gwamnati domin ci gaban al’umma. Ya ce, “Akwai bukatar mu kiyaye kayayyakin gwamnati da aka samar domin amfanin jama’a. A wasu lokuta, ana samun lalacewa daga hannun jama’a, wanda hakan kan jawo matsaloli. Wannan ne ya sanya muka kafa wannan kwamiti domin magance irin wadannan matsaloli.”
Dangane da rikice-rikicen da ke tsakanin manoma da makiyaya, Faskari ya bayyana cewa kwamitin zai duba al’amuran da suka shafi harkokin noma da kiwo tare da daukar matakan da za su hana tashe-tashen hankula.
Haka kuma, an ba kowanne daga cikin kwamitocin damar gayyato wasu masana ko kwararru da za su taimaka wajen cimma nasarar ayyukansu.
Daga karshe, Faskari ya yi kira ga al’ummar jihar da su bayar da hadin kai domin tabbatar da nasarar wannan tsari.