Tinubu Ya Naɗa Ogunjimi a Matsayin Mukaddashin Akanta Janar na Ƙasa
- Katsina City News
- 10 Dec, 2024
- 181
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a jiya, ya naɗa Shamseldeen Babatunde Ogunjimi a matsayin Mukaddashin Akanta Janar na Ƙasa (AGF).
Ogunjimi, wanda ya kwashe fiye da shekaru 30 yana aiki a hukumomin gwamnati, ya gaji Dr. (Hajiya) Oluwatoyin Sakirat Madein, wadda ta fara hutun gabatar da ritaya.
Kafin wannan naɗin, Ogunjimi ya kasance Darakta na Kudade a Ofishin Akanta Janar na Ƙasa (OAGF) da kuma Daraktan Kuɗi a Ma’aikatar Harkokin Waje. Haka nan, shi ƙwararren akawu ne, masani kan hana zamba, da kuma dillalin hannayen jari mai lasisi.
Shugaba Tinubu ya yaba da ƙwarewa da gogewar Ogunjimi, yana mai cewa zai tabbatar da ingantaccen tsarin tafiyar da baitulmalin ƙasa tare da goyon bayan sauye-sauyen tattalin arziki.
Dr. Madein za ta yi ritaya a ranar 7 ga Maris, 2025, bayan cikar shekarun ritaya na doka.