Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Katsina Ta Shirya Taron Wayar da Kan Jama’a Kan Cin Hanci da Laifukan Yanar Gizo
- Katsina City News
- 09 Dec, 2024
- 117
Hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe-korafen al’umma ta jihar Katsina, watau Katsina State Public Complaint and Anti-Corruption Commission, ta shirya taron wayar da kan al’umma karo na farko kan batun cin hanci da rashawa da kuma laifukan da suka shafi yanar gizo.
An gudanar da taron ne a ranar Litinin, 9 ga Disamba, 2024, karkashin jagorancin shugaban hukumar, Justice Lawal Garba, a dakin taro na ma’aikatar kananan hukumomi dake hanyar Kaita cikin birnin Katsina.
An shirya taron ne domin bikin ranar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 9 ga Disamba a kowace shekara don wayar da kan al’umma kan illar cin hanci. A yayin taron, masana daban-daban sun gabatar da kasidu masu muhimmanci akan cin hanci da rashawa da kuma laifukan yanar gizo. Daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi akwai Dr. Mukhtar Alkasim, Dr. Bashir Ruwan Godiya, da wasu manyan masana.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, wanda ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Jiha, Barrister Abdullahi Garba Faskari, shi ne ya kaddamar da bude taron a madadin gwamnatin jihar.
Taron ya samu halartar manyan baki, ciki har da wakiliyar alkalin alkalan jihar Katsina, wakilan kwamishiniyar shari’a, wakilin kwamishinan ’yan sanda na jihar, da wakilan sauran hukumomin tsaro. Haka zalika, kungiyoyin fararen hula da sauran kungiyoyin al’umma sun halarci taron, wanda ya zama dandalin tattaunawa kan hanyoyin dakile cin hanci da rashawa tare da tabbatar da gaskiya da adalci a jihar.