Ƴansanda Sun Daƙile Yunƙurin Yin Garkuwa, Sun Ceto Mutane 20 A Katsina
- Katsina City News
- 08 Dec, 2024
- 103
Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Katsina ta bayyana cewa ta samu nasarar daƙile yunƙurin garkuwa da mutane biyu a ƙaramar hukumar Jibia da Faskari, inda ta ceto mutane 20.
Kakakin Rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce wannan ceto na nuna jajircewa Ƴansanda wajen yaƙi da ‘yan fashin daji da kuma tabbatar da tsaron al’umma a jihar.
ASP Aliyu ya ce a ranar 7 ga Disamba, 2024, da misalin ƙarfe 7 na yamma, ‘yan fashin daji masu bindigogin AK-47 sun kai hari a kan wata mota da ke tafe daga hanyar Katsina – Magamar – Jibia kusa da kwanar Maƙera. ‘Yan fashin sun buɗe wuta da nufin yin garkuwa da fasinjojin motar.
Jami’an ‘Yansanda daga Jibia sun tashi da sauri suka ɗauki don dakatar da ‘yan fashin, wanda hakan ya tursasa su guduwa da raunuka, ba tare da cimma nasararsu ba. Dukkanin fasinjojin 10 da ke cikin motar an ceto su ba tare da wata matsala ba.
Ya ƙara da cewa yunƙurin garkuwa na biyu ya faru a Marabar Bangori a kan hanyar Funtua – Gusau a ƙaramar hukumar Faskari, inda aka kai hari ga wata mota ɗauke da fasinjoji 10. Jami’an ‘Yansanda sun isa wurin cikin hanzari suka yi musayar wuta, wanda ya dakatar da ‘yan fashin, duk fasinjojin an ceto su, sai dai daya daga cikin su ya samu rauni mai tsanani daga harbin ‘yan fashin.
Leadership Hausa