Fiye Da Daliban Sakandare 300 Daga Makarantu 7 A Shiyyar Katsina Sun Amfana da Tallafin Gidauniyar Lamidon Katsina
- Katsina City News
- 08 Dec, 2024
- 92
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
A ranar Lahadi, 8 ga watan Disamba, Gidauniyar Lamidon Katsina, wato *Lamido Foundation*, ta gudanar da wani shiri mai muhimmanci da ya yi nuni da goyon bayan karatun mata tare da inganta tsafta da kiwon lafiya. An rabawa dalibai mata fiye da 300 daga makarantu bakwai kayayyakin tsaftace jiki, a wani taro da aka shirya a dakin taro na makarantar 'Yanmata ta (WTC), Katsina.
Taron ya samu halartar manyan baki, ciki har da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, malaman kiwon lafiya, da masu fafutuka, wadanda suka gabatar da laccoci kan muhimmancin tsafta, hanyoyin kare kai daga kamuwa da cututtuka masu yaduwa, da kuma dabarun inganta rayuwar mata dalibai.
Da yake jawabi a madadin gidauniyar, Alhaji Jabiru Salisu Tsauri, babban shugabanta, ya bayyana dalilin shirya wannan tallafi, yana mai cewa:
> “Mun yanke shawarar bada wannan gudummawa ga mata ne duba da yanayin tattalin arziki da suke ciki. Ba wai don wadannan kayayyaki suna da yawa ba, amma suna da tasiri wajen rage bukatu da matsalolin da suke fuskanta. Mun kuma zabi mata saboda wannan batu na tsafta da lafiyar jiki ya fi shafar su.”
Ya kara da cewa, wannan tallafi yana cikin tsarin gidauniyar na inganta lafiyar jama’a ta hanyar wayar da kai da bayar da gudummawar kayayyakin tsafta. “Kwamitin kula da lafiya na gidauniyar, wato *Lamido Foundation Medical Team*, sun tsara wannan lacca ne domin kara wayarwa daliban kai kan muhimmancin tsafta da kulawa da lafiyar jiki,” in ji shi.
Tsauri ya yi godiya ga duk wadanda suka bayar da gudummawa wajen tabbatar da nasarar wannan shiri, ciki har da masu fada a ji irin su Nasiru Ala Iyatawa da Nana Yakubu, Shugabar makarantar WTC.
Dalibai da dama sun bayyana farin cikinsu kan tallafin da kuma laccocin da suka ce sun kara musu fahimta game da muhimman abubuwan da za su taimaka wajen inganta rayuwarsu, musamman wajen kula da lafiyar jiki da tsafta a kowanne yanayi.
Shirin, wanda aka yi a cikin tsari mai kyau, ya zama wani babban misali na yadda gidauniyoyi za su iya taka rawa wajen tallafa wa matasa da inganta rayuwarsu ta fannoni daban-daban.
Daga karshe, Gidauniyar Lamido ta bayyana aniyarta na cigaba da irin wadannan shirye-shirye, tare da karfafawa dalibai mata gwiwa domin su kasance jajirtattu a bangarorin ilimi da kiwon lafiya. Wannan shi ne kadan daga cikin irin gudummawar da gidauniyar ke bayarwa domin tallafa wa al’umma baki daya.