ADDINAN MUTANEN KASAR HAUSA KAMIN ZUWAN MUSULUNCHI.
- Katsina City News
- 07 Dec, 2024
- 211
Kamin bayyanar addinin Musulunchi a Kasar Hausa, Hausawa suna bin addinin su na Gargajiya Wanda suka gada kaka da Kakannin. Mafi yawan addinin mutanen Kasar Hausa a wannan lokacin shine bautar Iskoki da Bori da Tsahi da sauransu.
Babban dalilin da yasa alummar Kasar Hausa kirkira wadannan addini nai shine rashin wani tsayayyayen addini daga Allah a wancan Lokacin. Kadan daga cikin mabiya wadannan addinan a Kasar Hausa sun hada da
1. BAUTAR ISKOKI A DURBI-,TAKUSHEYI DAKE CIKIN KARAMAR HUKUMAR MANI TA JIHAR KATSINA.
Al' ummar Durbi- Takusheyi suna Bautar Iskoki a wancan Lokacin kamin bayyanar Musulunchi.Daga cikin shuwagabanin su na bautar Iskoki akwai Durbi, Ba-,tare- tare da sauransu. Durbi shine babban Limamnsu a wancan Lokacin ( Chief Priest). Mutane suna bi ta hannun shi idan suna neman wata bukata, ko taimako shi Kuma yayi masu iso ga iskokai da sauransu. Daga cikin Tsahin su na Durbi Takusheyi a wancan Lokacin akwai Kukar Katsi da Dutsin Batere tare da sauransu.
Akwai kuma Bori. Bori wani nauine na addinin Gargajiya na Hausawa, watau bautar Iskoki ko mutanen Boye, kamar yadda ta faru a Durbi Takusheyi. A gaba dayan Kasar Katsina a wancan Lokacin sun dogara ga addinin Gargajiya ( Bori) Yan Kasuwa, da Shuwagabanin da Talakawa kowa yayi imani da Bori da Tsahi Kuma shine abin dogarar su.
2. BAUTAR TSUNBURBURA A KANO.
A'ummar Kano kamin bayyanar Musulunchi sun dogare akan bautar wani Aljani Mai suna Tsinburbura. Kamar yadda ta faru a Durbi Takusheyi cewa Durbi shine babban limaminsu Kuma shine ke masu iso ga iskokai, to a kano wancan Lokacin anyi wani Mutum Mai suna Barbusheye. Barbusheye Mutum ne kakkarfa, Wanda yake zuwa ya wo Farauta ya kashe giwa ya daukota da hannun shi, har tsawon yini guda ya kawota gidanshi. To shi Barbusheshe shine yake isar da sakon Kanawa zuwa ga Aljanna Tsuburbura. Ita Tsinburbura Tana zaune a wata bukka cikin Dutsin Dala ta Kano. Barbushe shi kadai keda ikon shiga wajen Tsinburubura ya isar da sakon Kanawa a wancan Lokacin. Duk shekara zai shiga idan ya fito zai masu bayanin abin da zai faru a cikin shekara da sauransu. Irin wannan yanayinne al' ummar Kano suka cinchi kansu kamin bayyanar Musulunchi a Kasar Hausa.
3. BAUTAR DAN TALLE NA KAINA FARA ARNAN BIRCHI.
Kaina Fara wasu Arnane da yanzu suke zaune a Kauyen Goda Wanda yake kimanin tafiyar Kilomita biyu Yamma da Garin BIRCHI a Karamar Hukumar Kurfi ta Jihar Katsina. Kaina Fara Maguzawane wadanda suke aiwatar da al'adun gado na Gargajiya, amma wadanda suka sabawa kaidojin addinin Musulunchi. Suna Bautar wani abin bautane dake " DUTSIN DANTALLE". Duk shekara Kuma sukan hadu a gindin wannan Dutsin suyi bikin cika shekara. A lokacin wannan biki suna gudanar da wasu bukukuwa na al'adu, sannan a rufe bukin da Fadar abubuwan da zasu faru a shekarar Mai Kamawa. Har wayau kuwa suna daurin auren yayansu da giyane, sannan azo da kayayyakinsu na Tsahe Tsahe, da sauran al' adunsu.
Irin wannan yanayinne al'ummar Kasar Hausa ta samu kanta kamin bayyanar addinin musulunchi.
Acikin Karni na 14 zuwa na 15 mutanen Kasar Hausa suka karbi addinin Musulunchi ta hannun Larabawan Afirika wadanda suke shigowa Kasuwanci a Kasashen Hausa a wancan Lokacin. Duk da ansar Musulunchi da sukayi sai Kuma mutane suka rika chakuda addinin Musulunchi da addunin su na Gargajiya misali Bori da Tsahi. Misali yawancin mutane suna da Aljanin su a Gidajensu, Wanda suka bautamawa sannan Kuma a lokaci guda sun yarda da addinin Musulunchi.
A irin wannan yanayinne da al'ummar Kasar Hausa ta tsinchi kanta, ya jawo Kira akan Jihadin Musulunchi na Shehu Usman Danfodio na Karni na (19). Shehu yayi Kira da a Kaddamar da Jihadi, sannan Kuma a Jaddada addinin Musulunchi a gaba dayan Kasar Hausa.
Alh. Musa Gambo Kofar soro.