TATSUNIYA: Labarin Dan Tsintuwa

top-news

Akwai wata mata da mijinta, suna zaune a wani ƙauye. Sun ɗauki lokaci mai tsawo suna neman haihuwa, amma Allah bai basu haihuwa ba. Wata rana matar nan ta je gona, sai ta tarar da jariri a kan dutse. Ta ɗauki jaririn ba tare da ta san cewa ɗan aljani ne ba, sai ta kawo shi gida.  

Da mijinta ya ga jaririn, sai ya tambaye ta inda ta samo shi. Ta ce masa cewa ɗan tsintuwa ne. Sai mijinta ya ce, "Anya wannan jaririn mutum ne kuwa?" Matar ta ce ta sani cewa zai ƙi amincewa da ɗan, shi yasa ta kawo shi ba tare da tambaya ba. Don gudun zuciyar matarsa, sai mijin ya ce: “To, shi ke nan. Na yarda da shi, amma ki kula da shi sosai.”  

Suka ci gaba da rainon yaron. Kullum matar tana zuwa gona tare da jaririn, har ta samo wata yarinya da za ta riƙa kula da yaron idan ta fita gona. Kafin ta tafi, kullum tana dafa musu abinci ta bar musu.  

Amma da zarar ta fita gona, sai jaririn ya rikide ya zama babba, ya kama mai renonsa ya ɗaure, sannan ya cinye duk abincin, ya hana ta wani abu. Bayan haka, zai yi ta rawa da wasanni iri-iri. Idan ya lura matar ta kusa dawowa, sai ya sake komawa jariri, yana birgima a ƙasa yana kuka. Idan iyayen sun dawo, sai su yi tunanin cewa mai renon tana cutar da jaririn. Duk lokacin da mai renon ta so yin bayani, sai su dakatar da ita, suna ganin ita ke da laifi.  

Wata rana, wata tsohuwa makwabciyarsu wacce ba ta je gona ba ta hango abin da jaririn ke yi. Tsohuwar ta ga yadda jaririn ya rikide, ya ɗaure yarinyar, ya cinye abinci, sannan ya koma jariri kafin mahaifiyarsa ta dawo.  

Da tsohuwar ta ga abin, sai ta kira iyayen yaron ta faɗa musu duk abin da ta gani. Ta ce idan sun shirya fita gona, su zo gidanta su buya don su ga abin da jaririn ke aikatawa. Sun amince, suka shirya tafiya gona, amma sai suka buya a gidan tsohuwar. Da suka buya, sai suka ga jaririn ya rikide, ya ɗaure mai renonsa, ya cinye abinci, sannan ya yi rawa da wasanni kamar yadda tsohuwar ta faɗa.  

Da suka dawo gida, sai suka ƙi dukan mai renon, amma jaririn ya ci gaba da kuka. Mahaifiyar ta tafi gidan boka don neman mafita. Bokan ya ce idan sun koma gida, su ɗauko ɗan akuya kosasshe, sannan su fita zuwa wata babbar bishiyar kuka da ɗan jaririn. Idan suka isa, su yi dabara su gudu su bar jaririn da ɗan akuyan.  

Da gari ya waye, suka yi yadda bokan ya ce. Suka kai jaririn da ɗan akuya suka gudu daga wurin. Da jaririn ya ga shiru, sai ya kunce ɗan akuya, ya kama hanya zuwa cikin daji. Ba a sake ganin jaririn ba har abada.  

Darasin da Labarin Ke Koyarwa
1. Son zuciya ba ya kawo riba.  
2. Hakuri da godiya ga abin da Allah ya kaddara a rayuwa.  
3. Kwadayi ba ya haifar da alheri.  
4. Ƙaramar mage ba ta yin kyankyawa.  

Kurunkus.