"Kowa yasan akwai Matsaloli a Harkar koyarwa, Amma Munbiyo hanyar gyara " Inji Shugaban hukumar Malaman Makarantun jihar Katsina

top-news

"Kowa yasan Akwai Matsaloli a Yanda Koyarwa take daga Malaman Makarantu a Jihar Katsina, Amma Munbi hanyar Gyara" Sada Ibrahim Sada (TSB)

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 11/09/2023

Sabon Shugaban Hukumar Malaman Makarantu na jihar Katsina (Teachers'Service Board T.S.B)  Alhaji Sada Muhammad Sada, a Zantawarsa da Jaridar Katsina Times ya bayyana yanda ya samu hukumar da kuma Shirin da suke don ganin harkar Koyarwa ta ƙara inganta a jihar Katsina.

Alhaji Sada Muhammad Sada Tsohon Malamin Makaranta, Tsohon Malamin Makarantar Gwamnatin Tarayya FCE, Tsohon Ma'aikacin Hukumar Yiwa Ƙasa Hidima NYSC Tsohon Sakataren Ilimi na Dutsinma, sana a Yanzu yake Riƙe da Hukumar Kula da Malaman Makarantu na jihar Katsina, yace Tabbas Akwai Matsaloli a tsarin Koyarwa, kuma Kowa yasan halin da Ilmi da Malamai suke ciki, wannan ba wani abu bane boyayye ga jama'a. Yace "Akwai Abubuwa dayawa wadanda dole sai an tashi tsaye."

Yace, zamuyi Horo na Musamman domin ganin tsarin Koyarwar ya inganta, sana yayi kira ga Malaman Makarantu da suji tsoron Allah suyi abinda ya dace. Yace a ta nashi bangaren da yardar Allah ko wace kwarya zasu ajeta a gurbinta.

Sada ya bayyana cewa akwai tuntuba a Makarantu da zasuyi na bazata, don ganin yanda ake aikin koyarwa dole su sanya ido subi makarantu sako da lungu. Yace kuma "Ba zamuyi haka ba don tozarta wani, sai don kiyaye hakki akan abinda aka dorawa Malaman."

Shugaban hukumar ya yi kira ga Al'ummar jihar Katsina da su taya wannan sabuwar Gwamnati da Addu'a akan niyyarta, yace "Tabbas Gwamna Dikko Umar Radda da gaske yake akan kawo gyara ta kowane fanni, amma hakan ya danganta da Addu'a da samun hadin kan al'umma.

Akwai Cikakkiyar Tattaunawar ta Bidiyo da zamu sanya a Shafukanmu na Sada Zumunta.

www.katsinacitynews.com WhatssApp 07043777779, 08036342932. ☎️ 014548140

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *