MASU SHAGUNAN SAYAR DA MAGANI( PHARMACIST DA MEDICINE SHOPS) SUN KAI KOKE OFISHIN MAGAJIN GARIN KATSINA
- Katsina City News
- 06 Dec, 2024
- 179
Muazu Hassan
Ƙungiyar masu shagunan sayar da magani a jihar Katsina, sun kai koken Hajiya Farida Ibrahim mai wakiltar Pharmacist Council of Nigeria a jihar Katsina da laifin uzura masu da matsa masu da cin tara, kwashe masu magani a shaguna da kuma kulle masu shagunan sana'o'insu ba tare da bin ka'ida ba.
Ƙungiyar ta kai koken ne a ranar Alhamis 5 ga watan Disamba 2024 a ofis Magajin Gari da ke Ƙofar Soro Katsina.
Wanda ya wakilci Magajin Garin, Alhaji Abdu Wakilin Kudu, ya saurari 'yan ƙungiyar daki-daki inda suka bayyana irin uƙubar da suke sha a hannun Hajiya Farida Ibrahim, wadda ke sanya ido a shaguna da manyan kantunan sayar da magunguna a jihar Katsina.
Malam Abu Sufyan da ya yi magana a madadin ƙungiyar ya ce, suna goyon bayan aikin sa ido da bin ƙa'ida na tafiyar da manyan kantuna ko shagunan sayar da magani, amma suna ƙi, kuma ba su yarda da tsauri da kuma tsanani a wannan aikin ba. "Ba ka cewa sai an cika ƙa'ida ɗari bisa ɗari a hali da yanayin da ƙasarmu ke ciki."
Magajin Garin Katsina ya saurare su, kuma ya ce za su tattauna lamarin da ɗaukar matakin da ya dace na gayyatar Hajiya Farida Ibrahim domin samun wani zaure na fahimtar juna da aiki tare.
Binciken Katsina Times ya gano waɗannan kantuna da shagunan sayar magani sun samar da ɗimbin aiki ga matasa maza da mata masu yawan gaske a faɗin jihar Katsina.
Rufe su barkatai zai ƙara jefa jihar cikin wani halin rashin aikin yi da barazanar tsaro.
Bincikenmu ya gano ƙananan shagunan da ƙwararrun ma'aikatan lafiya kan buɗe a saƙo da lunguna na jihar na taimakawa wajen tallafin gaggawa ga masu ƙaramin ƙarfi marasa lafiya.
Katsina Times ta nemi jin ta bakin Hajiya Farida Ibrahim, wadda ta bayyana wa jaridun Katsina Times cewa duk abin da suke suna yi ne bisa ƙa'ida kamar yadda hukumar da ta turo ta Katsina ta ba ta umurnin ta yi.
Kuɗin da take caji na ƙa'ida ne da ake biya shekara-shekara, wanda ya kamata kowa ya biya duk ƙarshen shekara.
Ta ce tarar kuma da take ci duk tana cikin ƙa'ida kamar yadda yake a kundin Hukumar da take wakilta.
Haka zalika, Hajiya Farida Ibrahim ta jaddada cewa kwashe magani tana yi ne idan ya saɓa wa ƙa'idar da aka gindaya masa.
Ta tabbatar da cewa takan rufe wajen sayar da magani ne in ya saɓa ƙa'ida.
Ikirarin da masu kantunan da shagunan suka ce, aikin nata yana wuce iyaka.
A wata sabuwa, kantin sayar da magani na Lugga Clinic mai suna Lugga Pharmacy Ltd, ya maka Pharmacist Council of Nigeria da Hajiya Farida Ibrahim a kotu a bisa rufe masu wurin sayar da magani da aka yi.
Lugga Pharmacy sun kai ƙara kotu bayan rufe kantinsu da aka yi a ranar 28 ga watan Nawumba da ya gabata.
Kotu ta kalli cewa marasa lafiya a Asibitin za su cutu da wasu hujjojin ta ba da izinin buɗe wajen, da kuma sanya ranar 18 ga watan Disamba don cigaba da sauraron shari'ar.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779.080 57777762