"Hukuncin Kotu Na Ƙwace Mana Kujeri Wasan Kwaikwayo Ne, Idan Har Shari'a Na Aiki Zamu Ƙwata Abinmu" -Sanata Tsauri
- Katsina City News
- 11 Sep, 2023
- 767
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times. 11/09/2023
A Taron Manema Labarai da Tsohon Sakataren Jam'iyyar PDP, na Najeriya Sanata Umar Ibrahim Tsauri, Kuma tsohon Shugaban Yaƙin Neman Zaɓen Atiku da Lado a jihar Katsina, ya kira ya bayyana irin yanda aka shirya Kitimurmura da Kwace Kujerin da suka ci na 'Yan Majalisun Tarayya a karkashin jam'iyyar PDP. Sanata tsauri a Madadin Jam'iyyar ta PDP sunyi watsi da Hukuncin Kotun Ƙararrakin Zaɓen ta yi na bayyana Danmajalisar Tarayya daga Ƙaramar Hukumar Katsina Hon. Aminu Chindo a Matsayin wanda ba baida Takardun Firamare da, Ɗan Majalisar Kankia, Kusada a matsayin wanda shima bashi da Takardun, a yayin da Kotun ta bayyana Ƙananan hukumomin Safana, Batsari da Danmusa a matsayin Zaɓen da bai Kammala ba kuma Kotun ta Kwace ta bawa 'Yan Jam'iyyar APC. Yace Lallai wannan wasan Kwaikwayo ne, kuma Indai har Shari'a na Aiki a Najeriya to sai sun maido da Kujerinsu.
Da yake Amsa tambayoyin manema labarai, Tsauri ya bayyana wadanda sukai Anti Party a cikin jam'iyyar PDP da cewa suna nan suna nazarin yanda zasuyi da su tunda ba cewa sukayi sun bar jam'iyyar PDP ba. Taron da ya gudana a babbar Sakatariyar jam'iyyar PDP ta jihar Katsina a ranar Litinin ya samu halartar wasu daga cikin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a jihar Katsina.
Akwai cikakken Bidiyon a shafukan mu na Katsina Times a kafafen sada zumunta.
www.katsinatimes.com WhatssApp 07043777779, 08036342932, ☎️014548140