GWAMNA LAWAL YA GABATAR DA KASAFIN KUƊIN NAIRA BILIYAN 545 NA SHEKARAR 2025 GA MAJALISAR ZAMFARA, YA BA DA FIFIKO KAN TSAR:O, LAFIYA DA ILIMI
- Katsina City News
- 06 Dec, 2024
- 168
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ɗaukar wani tsari mai inganci wajen tafiyar da harkokin kuɗaɗen jihar.
A ranar Alhamis ne gwamnan ya miƙa wa Majalisar Dokokin Jihar Zamfara daftarin kimanin Naira Biliyan 545,014,575,000.00 a matsayin kasafin kuɗin shekarar 2025.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa a karon farko a Zamfara ma’aikatar lafiya ta ɗauki kashi 11% na jimillar kasafin kuɗin da aka tsara, wanda ya kai Naira 62,124,702,98.
Sanarwar ta ƙara da cewa, bangaren ilimi ya kai kashi 14% na jimillar kuɗaɗen, wanda kuma ya kai N79,664,861,461.
“Tsaro, wanda ya kai kwashi kashi 6% na adadin, ya kai N32,288,70,000. Noma ya kai kashi 6% wanda ya kai N34,716,18,000.”
Da yake gabatar da nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa kasafin kuɗin shekarar 2025 yana wakiltar taswirori na magance matsalolin da jihar Zamfara ke fuskanta.
Ya ce, “Hangen nesa ne na inganta makomar Zamfara. Bugu da ƙari, shaida ce ga ƙudirinmu na canja ƙalubale zuwa wadata, domin samun kwanciyar hankalin jama'armu.
“A cikin watanni 18 da suka gabata, mun samu gagarumin ci gaban kudaden shiga da ya kai kashi 240.44, wanda hakan ya sa darajar jihar mu ta ɗaga daga matsayi na 36 zuwa na 26 a tsarin samar da kudaden shiga na cikin gida na Nijeriya. Wannan shaida ce ta tsauraran matakan samar da kuɗaɗen shiga da kuma tsare-tsare da wannan gwamnati ke aiwatarwa don daƙile tabarbarewar kuɗaɗen shiga.
“Mun nuna jajircewar mu ga ɗorewar hakokin kuɗi ta hanyar samar da ingantaccen lissafin kuɗi, ingantattun tsarin tattara kuɗaɗe, da faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.
“Yayin da wannan nasarar ta zama abin yabo, yana da muhimmanci a lura cewa an samu matuƙar ci gaba a harkokin jihar. Za mu tabbatar da cewa masana'antu masu samar da kudaden shiga sun rubanya ƙoƙarinsu ta hanyar binciko duk hanyoyin da za a iya amfani da su da kuma ƙara damarmaki.
“Don hanzarta aiwatar da ayyukan ci gaban tattalin arziki da kuma samar da kyakkyawar makoma ga jama’armu, mun ƙaddamar da ayyukan da za su kawo sauyi tare da gagarumin ƙarfin da zai ƙarfafa tattalin arzikin jihar. Babban misali shi ne filin tashi da saukar jiragen sama na Gusau, wanda wannan gwamnatin ta samar domin inganta ayyukanmu.
“Muna ci gaba da aiwatar da muhimman ayyukan samar da ababen more rayuwa a hanyoyi, kiwon lafiya, aikin gona, raya karkara, da ilimi. An tsara waɗannan abubuwan ne don gina tattalin arziƙin da zai iya inganta rayuwar ’yan ƙasa.
“Mun tsayu kan ayyukan kawo sauyi a ma’aikatun gwamnati, wanda muka fara shi jim kaɗan bayan karbar mulki. Waɗannan gyare-gyaren na da nufin inganta ayyukan ma'aikatan jihar, da rage almubazzaranci, da tabbatar da amfani da dukiyar jama'a cikin gaskiya. Muhimmin al'amari na waɗannan gyare-gyare shi ne ƙididdige ayyukan gwamnati. Fitattun misalan sun haɗa da inganta Majalisar Zartarwar Jihar, rajistar filaye, samar da kuɗaɗen shiga, da tsarin tattara kuɗaɗe.
“Mun bullo da tsarin kasafin kuɗi mai aiki da kuma ƙarfafa hanyoyin sa ido kan kuɗi. Muna da nufin gina tsarin mulki na gaskiya da riƙon amana wanda zai sa jama'a su samu kwaciyar hankali da kuma ba da damar tafiyar da ci gaban zamantakewa da tattalin arziki.
“Shugaban Majalisa, mambobi, an tsara kasafin kuɗin shekarar 2025 sosai domin nuna muradin mu na samun ci gaban jihar Zamfara. Kamar kasafin kufin shekarar 2024, ya ba da fifiko wajen rarraba albarkatu cikin adalci, da kuma kafa ginshiƙin ci gaba mai ɗorewa. Tare da kokarin hadin kan masu ruwa da tsaki, ina da yaƙinin cewa za mu iya shawo kan ƙalubalen da muke fuskanta, mu samu ci gaban da mai ɗorewa a jihar Zamfara.
Gwamna Lawal ya ce, jimillar kiyasin kasafin shekarar 2025 ya kai N545,014,575,000.00, wanda za a kashe N151,680,000,000.00 ta hanyar al'amuran yau da kullum da kuma ₦393,334,575,000 ta hanyar ayyakan inganta jihar.