Sabuwar Jam'iyyar Arewa Ta Kunno Kai Don Kalubalantar Tinubu A Zaben 2027
- Katsina City News
- 03 Dec, 2024
- 378
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
Wata kungiya ta 'yan siyasa daga Arewacin Najeriya mai suna "Team New Nigeria (TNN) ta bayyana kudirinta na kafa wata sabuwar jam'iyyar siyasa domin Tumɓuke shugaba Bola Ahmed Tinubu daga mulki a zaben shekarar 2027.
Shugaban kungiyar na kasa, Modibbo Yakubu Farakwai, ya sanar da wannan mataki yayin kaddamar da kwamitin hadin kai a Kano a ranar Lahadi. Ya ce, rashin nasarar gwamnatin Shugaba Tinubu a bangarori da suka shafi tsaro, talauci, da rashin ci gaban ababen more rayuwa ne ya sa su yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar APC.
Ya kara da cewa, “Mun yi aiki tukuru tare da APC tun 2015 domin kwace mulki daga hannun jam’iyyar PDP amma abin takaici, mun yi matukar nadama kan wannan goyon baya da muka bayar.”
Kungiyar TNN ta ce ta riga ta fara tuntubar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) domin kaddamar da tsare-tsaren rajistar sabuwar jam’iyyar. "Mun riga mun tsara sunan jam’iyyar, kuma muna nan muna kokarin kammala dukkan shiri," in ji Farakwai.
Kungiyar ta kuma yi kira ga 'yan Najeriya, musamman matasan yankin Arewa, su tashi tsaye domin kawo canji mai ma'ana a siyasar kasar nan ta hanyar goyon bayan wannan sabuwar jam'iyya.