Cibiyar Fasaha ta KSITM za ta Shirya Babban Taro a kan Basirar Zamani ta Na'urar Artificial intelligence
- Katsina City News
- 01 Dec, 2024
- 242
Cibiyar Nazari kan Fasaha da Gudanarwa ta Jihar Katsina (KSITM) za ta shirya babban taro a karon farko, wanda zai tattauna kan yadda ake amfani da Basirar Na'ura ta Zamani, watau Artificial Intelligence a turance, a Ilimin Kimiyya da Fasaha da Lissafi (watau STEM).
Shugaban Hukumar Gudanarwar Cibiyar, Dr. Muttaqa Rabe Darma ne ya sanar da haka a wani taron manema labarai da aka yi a cibiyar da ke Katsina.
Ya bayyana cewa taron wanda aka shirya gudanar da shi a watan Afrilun ba'di, za a shirya shi ne tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Fasahar Sadarwa ta Jihar Katsina (KATDICT) da Jami’ar Alqalam da ke Katsina.
Ya sanar cewa daga yanzu, cibiyar za ta rika shirya manyan taruka biyu a kowane zangon karatu na shekarar, a kokarin mayar da KSITM wata cibiya da za ta rika jagorantar tattaunawa kan muhimman batutuwa na ilimi.
Hakazalika, Dr. Muttaqa Rabe ya bayyana cewa majalisar makarantar ta amince da kafa cibiyar bunkasa sana’o’i da hidimar al’umma, wacce za ta horar da kowane dalibi sana’o’in dogaro da kai.
“Manufar kafa cibiyar ita ce tabbatar da cewa kowane dalibi na KSITM ya samu kwarewa a fannoni a kalla hudu, wanda ya hada da fasahar zahiri da ta cikin na'ura.
“Dalibai kuma za su shiga cikin hidimar al’umma gadan-gadan domin muna so mu dasa musu kaunar al'uma a zukatansu, ta yadda zasu idan suka kammala cibiyar, zasu yi fice a fannin ilimi da halayya.
"Don a cinma wannan manufar, cibiyar za ta hada gwiwa da hukumomin da ke koya sana'o'i a matakin jiha da tarayya", in ji Dr. Muttaqa Rabe.
A fannin bunkasa samun kudaden shiga ga cibiyar, shugaban majalisar gudanarwar ya ce majalisar ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin Farfesa Muktar EI Kasim, domin nemo hukumomin da za a haɗa gwiwa da su don cinma wannan burin.
"Wannan shirin" ya ce "zai tallafa wa cibiyar wajen samun kudaden tafiyar da harkokinta a fannin nazari da manyan ayyuka, game da same mata hanyoyin cin gashin kanta".
Hakazalika, majalisar ta kara wa malamai 17 da ma'ikatan ofis 16 girma, kuma ta ba wasu ma’aikatan su takwas aiki domin inganta harkar karatu da karantarwa a cibiyar.
A barayi guda kuma, yayin da wa’adin shugaban cibiyar zai kare a ranar 12 ga watan Disamba, mataimakiyarsa, Dr. Hindatu Salisu Abubakar, za ta cigaba da gudanar da harkokin cibiyar har zuwa lolacin da za a nada wani shugaban.
“Hakazalika babu kowa a kan kujerar jami'in kudi na cibiyar, don haka za a wallafa tallar neman Masu coke wadannan guraben biyu bisa tsarin da hukumar NBTE ta shimfida, kuma za a rufe neman mukaman a ranar 20 ga Disamba, 2024", in ji Dr. Muttaqa.