Hukumar Kidaya ta Kasa Zata Yi Binciken Kan Mace-macen Mata Masu Juna Biyu da Kananan Yara
- Katsina City News
- 27 Nov, 2024
- 282
@ Katsina Times
Hukumar Kidaya ta Kasa tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya sun kaddamar da shirin nazari kan musabbabin yawan mace-macen mata masu juna biyu da kananan yara 'yan kasa da shekaru biyar wanda aka yi wa laƙabi da VASA.
Da yake karin haske ga manema labarai kan binciken, Kwamishinan Tarayya mai wakiltar jihar Katsina a Hukumar Kidaya ta kasa Engr. Bala Almu Banye ya bayyana cewa wannan zagaye na binciken VASA zai dora ne akan binciken da aka yi a baya daga shekarar 2014 zuwa 2019.
Ya ce manufar binciken ita ce samar da bayanai da za su taimaka wajen tsara manufofi da tsare-tsare na kiwon lafiya da nufin rage mace-macen mata da kananan yara.
Engr. Banye ya bayyana cewa binciken zai kuma samar da bayanai da gwamnati za su YI amfani da su domin fito da dabarun magance matsalolin da ke haifar da mace-macen yara ‘yan kasa da shekaru biyar da kuma matan da suka kai shekarun haihuwa.
Ya kara da cewa binciken ya biyo bayan kididdiga na bangaren da kiwon lafiya wanda aka gudanar a shekarar 2023 da 2024.
“Wannan binciken zai tattara muhimman bayanai kan mace-macen mata da kananan yara, tare da mai da hankali kan abubuwan da suka shafi zamantakewa da kiwon lafiya wadanda ke haifar da wadannan munanan asarorin.
“Wannan bayanan za su ba wa mahukunta damar magance matsalar mace-mace game da kirkiro manufofi da nufin inganta lafiyar mata da yara a jihar nan.
"Masu tattara bayanan za su ziyarci gidaje don yin hira da magidanta da matansu don tattara bayanan da za su taimaka mana mu fahimci musabbabin mutuwar mata da yara a yankunan mu," in Engr. Banye.
Kwamishinan Tarayyan na NPC ya yi bukaci sarakuna da shuwagabannin al'uma da su yi kira ga al’umma da su ba binciken hadin kai.
Ya kuma bukaci shuwagabanni a dukkan matakai da su bayar da goyon baya ga binciken tare da yin kira ga jama'a da su yi maraba da wadanda za su zo yin hira da su don tattaro bayanan.
"Muna kira ga jama'a da su ba da hadin kai ga masu tattaro bayanan domin za su yi musu tambayoyi kuma za su rubuta bayanan da za su ba su, domin amfani da su wajen binciken" in Engr. Banye.