TARIHIN SARAUTAR DURBI A MASARAUTAR KATSINA.
- Katsina City News
- 25 Nov, 2024
- 397
Sarautar Durbi tana daya daga cikin tsofafin Sarautu a Masarautar Katsina. Ita wannan Sarauta ta Durbi ta samo asline tun daga Sarakunan Durbi Takusheyi. Durbi Takusheyi sunan wani Gari, dake cikin karamar Hukumar Mani ta yanzu. Durbawa sunyi mulki a Durbi Takusheyi fiye da Shekaru dubu da suka wuce. To daga Durbawanne aka fara Sarautar Durbi, Kuma daga Sarautar Durbin ne aka samu sunan Durbi Takusheyi ma'ana Durbi Mai mulki a Kusheyi. Durbi a wancan Lokacin Yana daya daga cikin shuwagabanin Durbi Takusheyi, kusan ma ace shine babban su, na Tsahe Tsahe ko kuma Limaminsu, watau ( Chief Priest). Tun daga wannan lokacinne Sarautar Durbi Ta Fara. Mulkin Durbawa yazo karshe a cikin shekarar (1348) lokacin da akayi kokowa tsakanin Sarki Sanau, Sarki na karshe daga zuruar Durbawa da Muhammadu Korau, a lokacinne shi Korau ya kada Sanau ya yankashi a gaban Jamaaa ya Zama Sarkin Katsina Musulmi na farko acikin shekarar 1348.
Lokacin da Korau ya hau Sarauta a Katsina sai ya dauko Sarautar Durbi wadda Durbawa suka fara yi ya sanyata daga cikin Manyan Hakimai masu zaben Sarki a wancan Lokacin, domin suma arna su samu Wakilci.
A lokacin da Dallazawa suka amshi mulki daga hannun Habe/ zuruar Korau acikin shekarar 1806, sai Sarkin Katsina Malam Ummarun Dallaje ya Kara karfafa wannan Sarautar ta Durbi a inda ya dauko daya daga cikin Manyan Yayan shi watau Saddiqu ya nadashi Durbin Katsina Kuma Hakimin Mani acikin shekarar 1810. Durbi Saddiqu shine ya Zama Sarkin Katsina bayan rasuwar Sarkin Katsina Malam Ummarun Dallaje acikin shekarar 1835. Ance daga Sokoto Sarkin Musulmi ya zabeshi aka turo Galadiman Sokoto ya nadashi a Katsina. Bayan Durbi Saddiqu sai Kuma aka nada wani Badallajen Mai suna Durbi Fandiku daga shekarar 1836 zuwa 1860. Daga Durbin Fandiku sai Durbi Gidado, shi Durbi Gidado yana daga cikin zuruar Sullubawa, Kuma shine Mahaifin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko, shine Mutum na farko Wanda ba Dan Sarki ya samu Sarautar Durbi tun daga Habe har fulani. Durbi Gidado yayi Durbin Katsina Hakimin Mani daga shekarar 1860 zuwa 1883. Daga Durbi Gidado sai Durbi Yero, Durbi Yero Badallajene yayi Durbin Katsina daga shekarar 1883 zuwa 1888, shima yayi Sarkin Katsina bayan Turawan mulkin Mallaka sun tube Sarki Abubakar cikin shekarar 1905. Daga Durbi Yero sai Durbi Sada 1888 zuwa 1891, shima Basullubene. Daga Durbi Sada Sai Durbin Katsina Muhammadu Dikko 1891 zuwa 1906. Durbi Dikko Yana Durbi ne Turawan mulkin Mallaka suka zo Katsina acikin shekarar 1903, a lokacin Mulkin Sarkin Katsina Abubakar ( Badallaje). Lokacin da Turawa suka zo Katsina Sarki Abubakar da sauran Hakimai sun tarbesu a Kofar Yandaka inda aka sabkar dasu a Gidan Yarima dake Unguwar Yarima. Tun daga wannan lokacinne Sarki Abubakar ya hadasu da Durbin Katsina Muhammadu Dikko, yace yaje ya wakiltashi akan komi Turawa suke nema su biyo ta hennun shi, shine zai sanar da Sarki ma'ana Durbi Dikko ya zama Lieson Officer tsakanin Turawan Mulkin Mallaka da Sarkin Katsina Abubakar. Acikin shekarar 1905 ne Turawan mulkin Mallaka suka Tube Sarki Abubakar daga Sarauta akan wasu dalilai da suka faru, sai aka nada kanen mahaifin shi watau Malam Yero Sarauta acikin shekarar 1905. Shima Sarki Yeron an Turawa sun tube shi daga Sarauta acikin shekarar 1906. To daga nan ne sai suka ba Durbin Katsina Muhammadu Dikko Sarauta acikin shekarar 1906 aka nadashi acikin shekarar 1907. Durbi Dikko shine Sarki na farko a Katsina daga cikin zuruar Sullubawa Gidan Sarki Dikko. Bayan da Sarki Dikko ya Zama Sarki sai ya nada babban Dan shi Sarautar Durbi watau Durbi Muhammadu Sani ( Gidado) tun daga wannan lokacinne har zuwa yanzu Sullubawa zuruar Sarki Dikko sune suke Sarautar Durbi, Kuma duk a Garin Mani suka zauna, sai lokacin Sarkin Katsina Muhammadu Kabir Usman ya nada Alhaji Hamza Usman Sarautar Durbi ya maida hedikwatar ta a Jikamshi a maimakon Mani, bayan rasuwar Hamza Usman sai aka nada Alhaji Aminu Kabir a matsayin Durbin Katsina a Jikamshi. Yanzu Kuma an a lokacin Mulkin Sarkin Katsina Alhaji Dr. Abdulmumini Kabir Usman ya maida Sarautar Durbi a Garin Mani, ita Kuma Jikamshi ta koma Sarkin Gabas. Har dai ya zuwa yanzu Sullubawane ke rike da wannan Sarautar ta Durbi, Kuma Alhaji Babani Isah Mani shine Durbin Katsina na yanzu.
A halin yanzu Durbin Katsina Hakimin Mani Yana daya daga cikin Manyan Hakimman Katsina masu zaben Sarki ( King makers). Sauran sune Kaura, Yandaka, Galadima.
Alh. Musa Gambo Kofar soro.