Gwamnatin Jihar Katsina Ta Gabatar Da Kasafin Kudin Shekarar 2025.
- Katsina City News
- 25 Nov, 2024
- 238
Auwal Isah Musa, Katsina Times
Gwamnan jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Radda ya gabatar wa Majalissar Dokokin jihar Naira Biliyan 682 a matsayin kasasfin kudin shekarar 2025 mai kamawa.
Gwamna Radda a ranar Litinin 25 ga Nuwamnan 2024, ya tsaya a gaban Majalissar dokokin jihar, tare da gabatar mata da kudirin kasafin kudin shekarar 2025 har Naira Biliyan N682,244,449,513.87
A cewarsa, cikin muhimman abubuwan da kasasafin kudin zai fi ba wa muhimmanci, an ware Naira Biliya N157,967,755,024.36, wato kashi 23.15% na kasafin kudin a matsayin wadanda za a kashe waje ayyukan yau da kullum, tare da kuma Naira Biliyan N524,274,694,489.51 wanda yake kashi 76.85% na kasafin kudin a matsayin na manyan ayyuka.
Duk a cikin jawabin gabatar da kasafin, gwamnan ya bayyana kasafin kudin shekarar 2025 a matsayin wanda ya samu karin kashi 40% idan aka kwatanta da kasafin kudin shekarar da ta gabata, wanda ya ke a N200,535,619,501.61.
Kamar yadda gwamnan ya bayyanawa Majalissar, ya ce Ilimi shi ne kaso mafi tsoka a cikin muhimman abubuwan da kasafin kudin na 2025 ya kunsa; sai Noma, Ayyuka da Gidaje da Sufuri, Raya Birane da Bunkasa Rayuwar Al'umma, Ruwan Sha, Inganta Muhalli, Harkar Lafiya....ya zayyano su kamar haka:
1. Ilimi 14% (N95,995,873,044.70)
2. 2. Noma da Kiwo 12% (N81,840,275,739.70)
3. Ayyuka, Gidaje, da Sufuri 10% (N9,684,806,758.56)
4. Raya Birane Da Bunkasa Rayuwar Al'umma 9% (N58,728,146,293.72)
5. Ruwan sha 8%(N53,832,219,322.46)
6. Inganta Muhalli 7%(N49,835,521,799.25)
7. Harkar Lafiya 6%(N43,881,752,172.75)
8. Inganta Tsaro da Harkokin Cikin Gida 3%(N18,938,508,746.95).
9. Sauran abubukan da ka iya bijirowa 31%(N230,759,902,908.71).
Har wayau, Gwamnan ya bayyana gamsuwa da jin dadinsa kan yadda gwamnatinsa ta aiwatar da kasafin kudin shekarar 2024 mai shigewa cikin nasara.
Bugu da kari, gwamna Radda ya kuma zayyano wasu daga cikin muhimman nasarorin da gwamnatin tasa ta cimmawa a kasafin kudin shekarar 2024 mai shihewa, wanda suka hada da: Inganta Hanyoyi, Samar da Ababen More Rayuwa, Karin Samun Kudaden Shiga (IGR), da sauransu da kuma irin yadda suka gudanar da ayyuka da dama a bangarori daban-daban cikin nasara, inda ya bayyana haka a matsayin wadanda suka kawo wa jihar ci gaba a fannoni mabambanta.
Da da yake bayyana irin nasasrorin da gwamnatinsa ta samu musamman a bangaren tsaro wanda ya kawo jihar tangardar tattalin arziki a baya, gwamnan ya bayyana cewar, an samu nasarar tarwatsa ‘yanfashi da makami tare da dawo da zaman lafiya a kananan hukumomi da dama wadanda a baya suke cikin matsalar tsaro.
Da yake karkare jawabin gabatar da kasasfin kudin, Gwamna Radda, ya yi wa Majalisar da al'ummar jihar Katsina albishir da cewar " cikin kwarin gwiwa nake bayyana wa Majalissa kasafin kudin shekarar 2025 cewar zai bunkasar tattalin arziki da inganta rayuwar al'ummar jihar Katsina."
Ya kuma jaddada cewar "kasafin kudin shekarar 2025, an tsara shi ne bisa irin nasarorin nasarorin da aka samu a shekarar da ta gabata, da kuma kara kaimi ga ci gaban jihar Katsina a wannan kasasfin."