Ƙanin Kwankwaso ya kai Abba Gida-Gida kotu akan batun fili
- Katsina City News
- 23 Nov, 2024
- 15
Garba Musa Kwankwaso, ƙanin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya shigar da ƙara a gaban kotu kan ta hana gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar ɗaukar wani mataki a kan wani fili.
A cikin ƙarar har da hukumar KNUPDA da Kwamishinan Shari'a na jiha da sauran wasu mutane. Sai dai kuma, DAILY NIGERIAN ta jiyo cewa asalin filin na Kwankwaso ne ya baiwa wani kamfani mai suna WAECO, amma sai gwamna Abdullahi Ganduje ya ƙwace.
Daga baya sai hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jiha ta tabbatar da ƙwace filin, wanda ya ke a unguwar Kwankwasiyya City, bisa hujjar cewa lokacin da su ka bada filin WAECO bai yi rijista a matsayin cikakken kamfani ba.
Daga nan ne sai Ganduje ya dawo da kasuwar yan magani cikin wani bangare na filin. Shima Abba da ya hau, sai ya ƙi maidawa kamfanin WAECO filin, shine Garba Kwankwaso ya shigar da ƙara kan batun filin.
A umarnin da ya bayar, Mai Shari'a Usman Na'abba ya bada umarnin hana taɓa filin ga gwamnati sannan ya ɗage sauraren koken zuwa 27 ga watan Nuwamba.